Takarar sanata: APC ta gamsu da cancantar Inuwa Yahaya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE,

Jam’iyyar APC ta bayyana gamsuwarta da cancantar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bayan tantance shi domin tsayawa takarar kujerar Sanatan Gombe ta Arewa a zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da tantancewar ne a Plateau House da ke Abuja, inda kwamitin tantance ‘yan takarar Sanata na jam’iyyar ya karɓi gwamnan tare da duba takardunsa da cancantarsa domin shiga zaɓen.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya fito a matsayin ɗan takarar maslaha na APC a yankin Gombe ta Arewa, ya bayyana a gaban kwamitin tare da wasu gwamnoni da manyan jiga-jigan jam’iyyar da ke neman kujerun Sanata ƙarƙashin APC.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a.

Da yake jawabi yayin tantancewar, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yabawa gwamnoni bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa shugabanci da ci gaban jam’iyyar.

Ya ce jam’iyyar na da cikakken ƙwarin gwiwa kan gogewa da ƙwarewar shugabanci da waɗanda aka tantance suka mallaka, yana mai bayyana cewa sun cika dukkan sharuɗɗan kundin tsarin mulki da na jam’iyya.

“Dukkan waɗanda suka bayyana a gaban kwamitin sun cika ka’idojin da ake buƙata, saboda haka jam’iyya ta amince da su domin shiga takara,” in ji shi.

Ana sa ran Gwamna Inuwa Yahaya zai fafata a zaɓen Sanatan Gombe ta Arewa bayan fitowarsa a matsayin dan takarar maslaha na APC a yankin.

By ukarofi