Daga JOHN D WADA a Lafia
Ɗan takar gwamna a jihar Nasarawa Abubakar Giza ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamna a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar Zenith Labour Party inda yayi alƙawarin gina jihar da ayyukan cigaban kamar aiki wa matasa da tsaro da kuma kafa gwamnati mai kula da al’umma idan aka zaɓe shi.
Maigirma Abubakar Giza ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taro da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia wanda mambobin jam’iyyar ta Zenith Labor Party (ZLP) da ɗimbin magoya baya da masu ruwa da tsaki suka halarta.
Ya ce dalilin shigarsa jam’iyyar shi ne saboda aƙidun ta na adalci da daidaito da cigaba.
Ɗan takarar ya kuma jaddada cewa ZLP tana wakiltar haɗin kai da cigaban jama’a tare da kuma bai wa kowa dama daidai inda ya ƙara da cewa jam’iyyar ra kuma ƙunshi mutane ne ne masu haɗa kai da niyya ɗaya domin cimma burin da zai amfani al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya.
Ya jaddada muhimmancin bin tsarin dimokuraɗiyya yana mai cewa ba kamar wasu jam’iyyun da ke fuskantar rarrabuwa da shari’o’i masu tsawo ba ita dai ZLP ta tsaya haɗe domin kawo cigaba mai ɗorewa a Najeriya.
Alhaji Abubakar Giza ya cigaba da bayyana cewa “Kamar yadda wasu jam’iyyu ke fama da shari’o’i da rarrabuwa a kotu jam’iyyar Zenith Labour Party ta nuna bambancinta ba tare da irin hakan ba” inji shi.
Game da ƙudurorin da yake dasu da hangen nesansa kuwa Giza ya ce idan aka ba shi mulki zai ba da fifiko ne ga farfaɗo da tattalin arzikin jihar a duka matakai da samar da ayyukan yi domin ƙarfafa matasa da rage talauci a faɗin jihar da tallafa wa mata da jarin kasuwanci da inganta fannin noma da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da inganta fannin kiwon lafiya da Ilimi da sauransu.
Ya kuma soki jam’iyyar da ke mulki a jihar wato All Progressive Congress (APC) kan yadda take ba da fifiko ga tsarin ɓangaranci wato zoning a turance fiye da ƙwarewar ɗan takara da mutuncin sa inda yayi amfani da damar a ƙarshe yayi kira na musamman ga al’ummar jihar gaba ɗaya da su zaɓi mutanen da ke da mutunci da ƙwarewa da gaskiya da kuma masu kishin ƙasa na asali irinsa a shugabancin jihar a zaɓukan shekarar 2027 dake tafe.
Haka shima a nasa ɓangaren shugaban jam’iyyar na Zenith Labour Party na jihar ta Nasararsa Hon. Cletus Ogah ya bayyana kyakkyawan fata game da burin Abubakar Giza yana mai cewa jam’iyyar ta kuma bude wa kowa wannan damar
Ogah ya bayyana cewa masu neman takara masu shekaru 25 zuwa 29 za su karbi fom din sha’awa ba tare da biyan kudi ba.
