2027: Jonathan ya ƙalubalanci ƙarar neman hana shi tsaya wa takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya ƙalubalanci ƙarar da wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya shigar domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ta bakin lauyansa, Chris Uche, Jonathan ya roƙi Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ya yi watsi da ƙarar.

Lauyan ya bayyana cewa, sun shigar da takardun ƙalubalantar ƙarar tun ranar 5 ga Mayu, 2026, yana mai cewa an taɓa yanke hukunci kan irin wannan batu tun daga Babbar Kotun Tarayya har zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara.

A nasa ɓangaren, lauyan mai ƙarar, Ndubuisi Ukpai, ya ce an kawo masa sabbin takardu ne a kotu, don haka yana buƙatar lokaci domin mayar da martani.

Mai Shari’a Peter Lifu ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga Mayu domin sauraron ƙalubalen da Jonathan ya shigar da kuma ci gaba da shari’ar.

Kotun ta kuma umarci a aika da sammaci ga Independent National Electoral Commission (INEC) da kuma Babban Lauyan Tarayya, waɗanda su ma ke cikin waɗanda ake ƙara a shari’ar.

By Babaji