Taron HIBAF na bana zai tattauna kan rumbunan ilmi – Sada Malumfashi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Gidauniyar Open Arts wadda ke gudanar da Bikin Baje Kolin Littattafai da Fasahohin Hausa (HIBAF 2025) ta bayyana taken bikin wannan shekara da sunan “Rumbunan Ilimi. Wannan ya fito daga bakin shugaban gidauniyar Open Arts Foundation Sada Malumfashi a wani taron manema labarai da ya gudana, wanda wakilin Blueprint Manhaja ya halarta.

”Taken bikin na bana zai mayar da hankali ne kan muhimmancin adana ilimi da tarihin al’ummar Hausa, tare da amfani da zamani da fasahohin zamani wajen kiyaye su. Hakan na nufin tabbatar da cewa ilimin gargajiya da na zamani ba su lalace ba, face a haɗa su wuri guda domin amfanin al’umma.

Taron maneman labaran ya bayyana cewa tun da daɗewa Hausawa na da tsarin rumbunan ilimi a wurare daban-daban, musamman a cikin addini, al’adu da sana’o’i. Zuwa yanzu kuwa, fasahar dijital ta zama wata sabuwar hanya ta adanawa da yaɗa wannan ilimi. Hakan ya taimaka wajen bai wa matasa damar fahimtar tarihin Hausawa, da kuma kare mutuncin al’adun gargajiya daga gushewa.

Farfesa Ibrahim Malumfashi, ɗaya daga cikin jagororin gidauniyar ya jaddada cewa bikin na bana zai haɗa masana, marubuta, masu fasaha da ɗalibai domin tattauna hanyoyin inganta, adana ilimi a zamanin dijital. Haka kuma za a nuna dabarun amfani da kafofin zamani wajen tattara bayanai, adana su, da kuma yaɗawa ga duniya baki ɗaya domin cigaban al’ummar Hausa.

A ƙarshe, an bayyana bikin cewa zai zama wata babbar dama ta wayar da kai kan muhimmancin tsare ilimin gargajiya da na zamani. Gidauniyar Open Arts ta kuma jaddada cewa HIBAF 2025 zai bayar da gudunmawa sosai wajen raya ilimin Hausa, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masana, masu fasaha da duk masu ruwa da tsaki a fagen ilimi da al’adu.

Taron na bana zai gudana a ranakun 18-20 ga wannan wata na Disamba a ɗakin taro na Arewa House da ke garin Kaduna.

By ukarofi