
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin saman yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda matuƙa biyu suka tsira daga cikin jirgin kafin ya kama da wuta.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa jirgin ya tashi ne daga sansanin sojin sama na Kainji.
Haka kuma al’ummar yankin sun ce abin ya faru ne misalin ƙarfe 4:10 na yamma, inda aka ga wutar da ta tashi daga wurin da jirgin ya faɗi.
Wani shaida mai suna Lukman Sulaiman ya tabbatar wa manema labarai matuƙa jirgin sun yi nasarar tsere gabanin ya kama da wuta.
An ga wani faifan bidiyo da ke nuna yadda jirgin yake ci da wuta ɗauke da tarin hayaƙi, kamar ƴan ƙauyen suek kallo daga nesa.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, NAF ba ta fitar da sanarwar ta musamman akan al’amarin ba.
