Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Da safiyar Asabar ɗin nan maigirma tsohon ministan shari’a kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓe mai zuwa Alhaji Abubakar Chika Malami ya ƙaryata zargin sa da hannu a cikin harkokin ta’addaci da wata jaridar Daily Trust ta wallafa a shafin ta na sada zumunta kwanan nan kamar haka “Binciken Operation Service Wide (OSW) – wanda Buhari ya shirya tun 2021 – ya gano alaƙar wasu manya da B0k0 Háram, ciki har da waɗanda ake zargi suna tallafawa ta’addanci.” inda aka alaƙanta waɗansu mutane guda biyu da ba a bayyana sunayen su ba da aka ce suna da alaƙa da tsohon ministan.
Abubakar Malami SAN, ya bayyana matsayinsa inda ya ƙaryata zargin tallafawa ta’addanci, ya kuma tabbatar da gudummawar da ya bayar wajen gyaran dokokin AML/CFT da fiitar da Nijeriya daga jerin ƙasashe na FATF.
Ya ce ” An ja hankalina kan wani labari da aka wallafa kwanan nan wanda aka ambaci sunana a cikin zarge-zargen tallafa wa ta’addanci da kuma wasu “dangantaka” da mutanen da aka bayyana a matsayin waɗanda ake zargi da aikata ta’addanci ko kuma masu taimaka wa ayyukan ta’addanci.
Don haka, a cikin neman gaskiya, adalci da kuma tantance bayanan tarihi, na ga ya dace in yi waɗannan bayanai”
Da farko, ina bayyanawa a fili kuma ba tare da wata shakka ba cewa a ko wane lokaci ban taɓa zarguwa, gayyata, tambaya, bincike ko gurfanarwa daga kowace hukuma ta tsaro, ‘yan sanda, mai sa ido, ko cibiyar leken asiri—cikin gida ko wajen Najeriya—dangane da zargin tallafa wa ta’addanci ko makamancin hakan.
Na biyu, kuma shi wannan babban hafsan soja mai ritaya da aka danganta labarin da shi ya bayyana a fili cewa bai taɓa zargina ba, ko wasu mutanen da aka ambata, da tallafa wa ta’addanci. Abin da ya faɗa kamar yadda aka ruwaito ya tsaya ne kawai kan zargin cewa wasu mutanen da ake tuhuma suna da wani nau’in hulɗar kasuwanci ko ta ofis da wasu mutane. Wannan muhimmin bayani, abin takaici, ya ɓace a cikin taken jarida da yadda aka shirya labarin, wanda hakan ya iya jawo kuskuren fahimta ga jama’a kuma ya ba wasu abokan hamayyata damar amfani da shi wajen ƙirƙirar mummunar fahimta da nufin cewa ina da alaƙa da tallafa wa ta’addanci” In ji shi”.
Ya ƙara da cewa tallafa wa ta’addanci babban laifi ne mai barazana ga tsaron ƙasa da rayuka. Duk wani yunƙuri ta hanyar zargi kai tsaye ko a kaikaice na danganta mutum da irin wannan laifi dole ne ya kasance cikin hujjoji masu tabbas, tsarin doka da sahihan bayanai, ba zato ko kuma danganta wa ta banza. Yin amfani da ƙawancen aiki na doka ko na ofis a matsayin dalilin zargin tallafa wa ta’addanci abu ne mai cutarwa da rashin adalci.
