Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina,Dikko Umaru Raɗɗa ya faɗi haka a garin Jibiya lokacin da ya kai ziyarar aiki a ƙaramar hukumar Jibiya.
Ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa da sake gina asibitin Jibia gaba ɗaya, domin rage cunkoso na marasa lafiya da ke dogaro da cibiyar wajen samun kulawar lafiya.
Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnati ta ɗauki matakin faɗaɗa asibitin ne bayan wani buƙatu da ɗan madamin Katsina kuma Hakimin Daddara, Alhaji Usman Usman Nagoggo, ya gabatar, inda ya roƙi a faɗaɗa gina muhimman gine-ginen gwamnati da ’yan bindiga suka lalata.
Ya tabbatar wa shugabannin gargajiya na Jibia cewa aikin sake fasalin asibitin zai fara ba da jimawa ba, yana mai cewa inganta cibiyoyin lafiya na daga cikin ginshiƙan tsare-tsaren gwamnatinsa na inganta lafiyar al’umma.
Haka kuma yayin ziyarar, gwamnan ya ƙaddamar da wani tallafi ga al’ummar yankin domin ƙarfafa tattalin arziki mai faɗi da shugaban ƙaramar hukumar Jibia, Alhaji Surajo Ado, ya samar.
Kayayyakin sun haɗa da injinan nika 100, injinan dinki 100, injinan yin taliya 100, da injinan nika barkono 100 domin tallafa wa mata da ƙananan ’yan kasuwa masu harkar sarrafa abinci da sana’o’in gida.
Sauran kayayyakin sun haɗa da: adaidaita sahu 50, keken hawa 50, babura 50 ga wasu matasa, kayan ɗaki ga amare marayu 10, tallafin kuɗi ₦20,000 ga matasa maza da mata 609, kayan gyaran gashi 100, da sababbin babura 17 ga dukkan shugabannin kauyuka a ƙaramar hukumar.
Gwamna Raɗɗa ya yaba da Jibia bisa kasancewa jagora wajen tattaunawar samar da zaman lafiya da ’yan bindiga, inda ya ce jarumtar su wajen shiga tattaunawa ta taimaka wajen samun zaman lafiya a yankin.
“Da haɗin kai, addu’a, da fahimtar juna tsakanin gwamnati da al’umma, muna fara ganin canjin daya ke nuni da samun zaman lafiya,” in ji Dikko Raɗɗa.
Ya roƙi shugabannin addini da da su ci gaba da amfani da huɗubar Juma’a don ƙara yawaita addu’o’in samun ɗorewar zaman lafiya a faɗin jihar.
Hakimin Daddara, wanda ya yi magana a madadin hakiman Jibia da Daddara, ya roƙi sake gina hanyoyin Katsina–Bugaje–Gangara da Gurbi–Shimfida domin inganta zirga-zirga da dawo da al’amura yadda suka saba a yankunan da matsaloli rashin tsaro suka taɓa a baya.
Daga baya Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da sabuwar ɗakin haihuwa da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Jibia/Kaita, Hon. Sada Soli, ya gina, sannan ya duba aikin gine-ginen ɗakin jin daɗi da shugaban ƙaramar hukumar Jibia ya fara.
Haka kuma ya ƙaddamar da ofishin shugaban ƙaramar hukumar da aka gyara da ɗakin taro da aka inganta.
Da yake jawabi ga jama’a a sakatariyar ƙaramar hukumar ta Jibia, Gwamna Raɗɗa ya yaba wa ɗan majalisar tarayya da shugaban ƙaramar hukuma kan ingantaccen gudanar da aiki, tare da nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ci gaban al’umma.
A cikin tawagar gwamnan akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, Sanatan Katsina ta Tsakiya, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua,da Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dutsi da Mashi, Hon Salisu Yusuf Majigiri, sai ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Jibia/Kaita Hon. Sada Soli.
