Tashar sararin samaniyar Sin za ta kasance “gida cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama

Daga CMG HAUSA

Da misalin ƙarfe 3 da minti 37 na yammacin jiya Litinin 31 ga watan Oktoba, ƙasar Sin ta yi nasarar harba ɓangare na uku, na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya.

Sa’an nan, bayan kimanin minti 8, ɗakin gwaje-gwaje na Mengtian ya rabu da rokar Long March-5B, ya kuma shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara.

Lamarin da ya nuna cewa, yawan ɗakunan gwaje-gwaje na tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, sun ƙaru daga guda biyu zuwa guda uku, waɗanda za su kasance tamkar “siffar T”, matakin dake ƙara kusanto ga aikin kammala tashar.

Aikin gina tashar binciken sararin samaniyar ya kasance muhimmin mataki a aikin sararin samaniyar ƙasar Sin, inda ƙasar Sin ke tsayawa tsayin daka wajen raya aikin bisa manufofin amfani da albarkatun sararin samaniya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adalci don cimma moriyar juna, da kuma bunƙasa harkokin dake da nasaba da hakan cikin haɗin gwiwa.

Kana, cikin tarihin bil Adama, tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, ita ce tasha ta farko da aka buɗe ga dukkanin mambobin MƊD.

A halin yanzu, ƙasar Sin ta bayar da izinin yin gwaje-gwaje a tasharta ga shirye-shirye guda 9, da ƙasashe guda 17, da kamfanoni guda 23.

Lamarin da ya nuna aniyar ƙasar Sin ta inganta dunƙulewar dukkanin bil Adama a fannin haɓaka aikin sararin samaniya.

Albarkatun sararin samaniya sun zama albarkatu ga dukkanin bil Adama, ya kamata a yi amfani da su wajen tallafawa dukkanin bil Adama.

Bayan an kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin, za a shiga matakin amfani, da kuma raya tashar na tsawon shekaru 10.

Kana, kafin ƙarshen shekarar bana, ƙasar Sin za ta kuma harba kumbo mai ɗauke da kayayyaki na Tianzhou mai lamba 5, da kumbo mai ɗauke da mutane na Shenzhou mai lamba 15, ta yadda ’yan sama jannati guda 6 za su yi aiki tare cikin tashar.

Ana da imanin cewa, a nan gaba, tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin za ta kasance “sabon gida cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama, inda za su gudanar da aikin binciken sararin samaniya cikin haɗin gwiwa.

Cikin tashar, ’yan sama jannati na ƙasar Sin da na kasashen waje, za su ba da gudummawar binciken sararin samaniya cikin haɗin gwiwa, yayin da ake karfafa aikin yin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana.

Mai Fassarawa: Maryam Yang