Ci gaban ƙasar Sin nasara ce ta duniya ba ƙalubale ba

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Lamuran da suka faru a duniya, sun nuna mana cewa, nasara da ci gaban duniya, sun dogara ne da haɗin gwiwa da taimakekeniya da kuma moriyar juna tsakanin ƙasa da ƙasa. Don haka, ƙyashi ko adawa da ci gaban wata ƙasa, ba zai taba amfanawa duniya ba.

Yadda ƙasashen yammacin duniya ke alaƙanta ƙasar Sin da kalmar “barazana” ko “ƙalubale”, abun damuwa ne ga zaman lafiya da ci gaban duniya.

Nasarar Sin, nasara ce ga ɗaukacin duniya, bisa la’akari da yadda karuwar tattalin arzikinta ko nasarori ko fasahohi ko ci gabanta ke shafar duniya baki ɗaya.

Yayin da suke tattaunawa a makon da ya gabata, sabon Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da shugaban Amurka Joe Biden, sun bayyana cewa, za su haɗa hannu wajen magance “ƙalubalen ƙasar Sin”.

Shi ma sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya bayyana ƙasar Sin a matsayin barazana, yayin da yake neman Amurka ta ƙara taimaka wa Ukraine a rikicinsu da Rasha.

Ba mu taba jin inda aka ce ƙasar Sin ta kitsa juyin mulki a wata ƙasa ba, haka ma ba mu taba jin cewa Sin ta yi mulkin mallaka ko ci da gumin wasu ƙasashe ba.

Ƙasar Sin ba ta taba girke sojojinta a wata ƙasa da sunan kare kanta ba, har ila yau, ba mu taba jin inda aka ce ta yi kutse ko katsalandan cikin harkokin wata ƙasa ko cusawa wata ƙasa manufofinta ba. To ya aka yi ta zama barazana ko kalubale?

Ko kaɗan, bai kyautu waɗannan shugabanni su riƙa ayyana Sin a matsayin barazana ba, domin hakan, bata suna ne, suna nema jan Sin cikin rikicin da su ne suka rura wutar ta.

Neman ɗora wa Sin laifi, ba zai kawar da hankalin duniya daga ainihin waɗanda ke da alhakin haifar da rikicin ba. Ƙasar Sin ba ta taba sauya matsayarta game da batun Rasha da Ukraine ba, wadda ita ce hawa teburin sulhu.

A ganina, yadda ake alaƙanta ta da barazana ko ƙalubale, ba komai ba ne face adawa da ci gabanta da nasarori da farin jininta a idon duniya, wanda kuma ta same su ne ta sahihiyar hanya.

Don haka, yunkurin shafa mata kashin kaji, ba zai haifar da komai ba illa bayyana ainihin masu laifi.