ATSSSANA ta dakatar da aiki a Filin Jirgin Saman Murtala saboda korar mabobinta daga aiki

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata ma’aikatan Babban Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Legas suka yi zanga-zanga tare da rufe ƙofar shiga filin
domin nuna rashin jin daɗinsu dangane da korar wasu jagororinsu da aka yi daga aiki.

Wannan al’amari ya jefa matafiya da suka kasance a filin jirgin a wannan lokaci cikin mawuyacin hali kasancewar masu zanga-zangar sun dakatar da komai a filin jirgin.

Jiragen da suka kasa samun sararin tashi a wannan lokaci sun haɗa da Ibom Air da Air Peace.

Sanarwar da ƙungiyar ma’aikatan (ATSSSAN) ta fitar, ta nuna kora daga aikin ta shafi wasu jagororin ƙungiyar ne saboda sun nemi a biya ma’aikatan haƙƙinsu.

Don haka ƙungiyar ta ce mambobinta za su shiga yajin aiki a nan Filin Jirgin Saman Murtala har sai sun cimma buƙatarsu.