Lokaci ya yi da za mu canza yadda muke tunkarar lamarin ‘yan bindiga

Daga MUS’AB ISA MAFARA (phd)

Na ga bidiyon ‘yan matan Furfuri da aka sace, an ce sun yi watanni a hannun waɗannan ‘yan ta’adda. Abun akwai ƙona rai. Allah Ya ba su mafita Ya sa kaffara.

Na san idan mutum bai samu kansa a cikin wani hali ba ba zai taɓa sanin ya lamarinsa zai kasance ba. Amma ni kullum tunanina wai dole ne ka bi ɗan bindiga zuwa daji don kawai yana da bindiga kai ba ka da ita?

Ƙarshen ta dai ya kashe ka in ba ka je ba, to ba gara mutuwa da halin da suke sa mutane a ciki ba? Sannan ita mutuwa a irin wannan hali ai shahada ce.

Hadisi ya zo daga Manzon Allah (SAW) Ya na cewa: “Duk wanda aka kashe wajen kare dukiyar shi, ya yi shahada. Duk wanda a ka kashe wajen kare addinin shi, ya yi shahada. Duk wanda aka kashe wurin kare rayuwarsa, ya yi shahada. Duk wanda aka kashe wurin kare iyalinsa, ya yi shahada.”

A wani hadisi na daban kuma, “wani mutum ya zo ya tambayi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, me kake gani idan mutum ya zo ya ƙwace min dukiya? Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, kada ka ba shi.

Mutumin ya ce to idan ya yaƙe ni fa? Manzon Allah Ya ce, ka yaƙe shi. Mutumin ya ce to in ya kashe ni fa? Manzon Allah Ya ce, ka mutu shashidi. Mutumin ya ce to idan na kashe shi fa? Manzon Allah Ya ce, yana cikin wuta.”

Ba wai ina ganin laifin waɗanda ake sacewa ba tun da ban tava shiga cikin irin halin da suka shiga ba, balle na san ni ya zan yi ba. Sai dai a Musulunce, sai na ga bai kamata kawai wani ya gargaɗa ka cikin daji kawai saboda yana da bindiga ba. Bai kamata wani ya qwaci dukiyarka ko ya ɗauki iyalinka ba, kuma kana tsaye kana kallo.

Bari in sake maimaitawa. Ba ina ganin laifin waɗanda aka sace ba ne ko kuma laifin iyaye da ‘yan uwansu ba. Sannan ni ban ga laifin mutum ya biya fansa ya karvo ɗan uwansa wurin varayi ba. Sai dai ina ganin kamar lokaci ya yi da za mu canza yadda muke tunkarar lamarin nan. Ka samu makaminka, ko da takobi ne ka ajiye. Duk wanda ya nemi rayuwarka ka nemi tasa. Ko ka kashe shi ko ka yi shahada.

Allah Ya ba su mafita Ya ba iyayen haƙuri Ya kuma hore musu hanyar dawowa da ‘ya’yansu gida. Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan bala’i da muke ciki.