Tashin hankali ya sake ɓarkewa a Afirka ta Kudu yayin da zanga-zangar ƙyamar baƙi ke ƙara ƙamari

Spread the love

Fargabar sake ɓarkewar rikicin kyamar baƙi ta mamaye sassa da dama na Afirka ta Kudu bayan dubban masu zanga-zanga sun mamaye titunan manyan biranen ƙasar ranar Talata, don nuna adawa da ci gaba da zaman baƙin haure ba bisa ƙa’ida ba.

Zanga-zangar, wadda ƙungiyoyin masu adawa da shige da fice irin su March and March da Operation Dudula suka shirya, ta zo ne bayan cikar wa’adin da aka bai wa baƙin hauren da ba su da takardun zama su fice daga ƙasar. Lamarin ya haifar da tashin hankali a biranen Johannesburg, Pretoria, Durban da sauran yankuna da dama.

Ko da yake masu shirya zanga-zangar sun dage cewa manufarsu ita ce yin adawa da baƙin hauren da ke zaune ba tare da izini ba, lamarin ya haifar da firgici tsakanin dubban ‘yan ƙasashen waje, har da waɗanda ke da cikakkun takardun zama a ƙasar.

Sakamakon haka, mutane da dama sun rufe shaguna da wuraren kasuwancinsu, yayin da wasu iyalai suka tsere zuwa majami’u, ofisoshin jakadanci da wuraren ba da mafaka domin neman kariya daga yiwuwar hare-hare.

Mahukuntan Afirka ta Kudu sun baza ɗaruruwan jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro masu ɗauke da manyan makamai a wuraren da ake ganin za su iya fuskantar tashin hankali, domin kauce wa maimaita rikice-rikicen kyamar baƙi da suka yi sanadin mutuwar mutane da lalata ƙadarori a shekarun baya.

Sai dai duk da wannan mataki, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu wasu hare-hare daban-daban a wasu al’ummomi, inda aka yi awon gaba da kayayyaki, aka tsoratar da jama’a, tare da kai farmaki kan shaguna da kasuwancin da baƙin haure ke gudanarwa.

A wasu sassan lardin Gauteng kuwa, jami’an tsaro sun shiga tsakani domin tarwatsa wasu gungun mutane da suka fara nuna alamun tashin hankali.

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa kowa na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, amma ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’in tashin hankali, barazana ko farmaki kan baƙin haure.

Gwamnatin ƙasar ta kuma sake nanata cewa yaƙi da aikata laifuffuka ya kamata ya kasance aikin hukumomin tsaro da na shari’a, ba wai jama’a su ɗauki doka a hannunsu ba.

By ukarofi

Leave a Reply