Tauraron Brazil da Real Madrid, Vinicius ya samu rauni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar ƙwallon ƙafar Brazil da Real Madrid na fuskantar matsalar babban giɓi sakamakon rauni da ɗan wasa Vinicius Junior ya samu.

Wannan a’amari na zuwa ne yayin da ‘yan wasan Brazil suke atisayen shirin gabanin wasan kawance da ƙasar za ta yi da Croatia.

Hakan na zuwa ne tun bayan wasan da Faransa ta casa Brazil da ci 2 da 1 a makon da ya gabata inda Vinicius soma fama da ciwon damtse.

An ga yadda ‘yan wasan Brazil suka fito atisaye a Orlando a jiya Asabar ba tare da ɗan wasan ba.

Hakan ya sa aka ɗauki matakin dakatar da shi ishiga atisayen ne domin kiyaye lafiyarsa don kada al’amarin ya faɗaɗa.

Rashin Jr acikin ‘yan wasan Brazil babbar matsala ce domin gabanin haka ma ‘yan wasa Wesley da Rafinha sun samu rauni.

By Babaji