Kwankwaso da magoya bayansa na shirin koma wa ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026 ne ake sa ran jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar adawa ta ADC.

Rahotanni daga sahihan majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kano na shirin ficewa daga jam’iyyarsa ta NNPP tare da koma wa ADC.

Majiyoyin sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa wannan mataki na zuwa ne bayan shafe makonni ana tattaunawa tsakanin Kwankwaso, ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya, da shugabannin jam’iyyar ADC domin cimma matsaya.

Ana kallon wannan sauyi a matsayin babban ci gaba a siyasar Nijeriya, musamman duba da tasirin Kwankwaso da magoya bayansa a arewacin ƙasar.

Idan har wannan sauyi ya tabbata, ana sa ran zai ƙara sauya tsarin siyasar jam’iyyun adawa gabanin zaɓukan 2027 da ke tafe.

By Babaji