

Daga BELLO A. BABAJI
Biyo bayan doke mai riƙe da kofin, Barcelona da ci 1 da 0, tawagar mata ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lashe kofin gwarazan Nahiyar Turai, wato UEFA Women’s Champions League a karo na biyu.
An buga wasan na ƙarshe ne a Filin Estádio José Alvalade dake Birnin Lisbon a ƙasar Portugal 🇵🇹.
Ƴar wasa Stina Blackstenius ce wadda ta zura ƙwallon a minti na 74, lamarin da ya bai wa Arsenal nasarar lashe kofin tun bayan da ta lashe a shekarar 2007 lokacin da ake kiran sa da UEFA Women’s Cup.
Ƙungiyar Barcelona ce ta lashe kofin a jere kafin yanzu kuma ta ke harin samun na huɗu.
Wannan shi ne karo na biyu da ake doke ta a wasan ƙarshe na gasar tun da Lyon ta doke ta da ci 3 da 1 a shekarar 2022.



