Ɗangote ya tallafa wa mata ’yan kasuwa a Binuwai da Naira 100,000 kowannen su

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani gagarumin ci gaba ga mata masu kasuwanci a Nijeriya, Kamfanin Siminti na Dangote ya baiwa mata ‘yan kasuwa da ke zaune a jihar Benuwai tallafin kuɗaɗe, ta yadda za su zurfafa harkokin kasuwancin su.

Shirin ƙarfafa matan ya zo ne watanni bayan da kamfanin simintin Dangote da ke Gboko ya ƙara biyan kuɗaɗen alawus-alawus ga ɗaliban yankunan da ke karɓar baƙuncinsa da sama da kashi 100 cikin 100.

Da yake jawabi a wajen bikin a ranar Laraba a Gboko, Shugaban Rukunin Kula da Ayyukan Jama’a na Kamfanin Simintin Dangote, Mista Wakeel Olayiwola ya ce, “Ta hanyar wannan tsari, zababbun mata ‘yan kasuwa a yankunan da suka karɓi baƙuncin sa za su sami tallafin N100,000 kowannensu don ƙarfafawa da faɗaɗa kasuwancinsu.

“Tallafin kuɗin na da nufin bunƙasa kasuwancin gida a matakin farko, da ƙarfafawa ‘yan kasuwa mata da jari don bunƙasa ayyukansu. Kowace mai cin gajiyar za ta yi amfani da kuɗaɗen don magance takamaiman buƙatun kasuwancin ta, daga sayen kaya zuwa bunƙasa kayan aiki, tare da samar da ingantaccen tasiri na tattalin arziki a cikin al’ummominsu.”

Wakeel ya ce: “Lokacin da mata suka yi nasara a kasuwanci, suna saka hannun jari ne a cikin ilimin iyalansu, kiwon lafiya, da walwala, suna karya tsarin talauci tare da haifar da tasirin mai kyau a cikin al’ummomin su.”

Ya ce, shirin zai ba wa mata damar samun ƙarin kuɗin shiga don ciyar da iyalansu, rage dogaro da mazajensu fiye da kima.

Ya ce kuɗin tallafi ne kuma ba za a mayar da su ga simintin Dangote ba.

A cewarsa, sarakunan gargajiya na: ƙuarry, Tse-Kucha, Amua, Mbazembe, Mbatur da Pass Brothers sun karɓi baauncin al’umma, inda kuma kwamitin Tuntuba na Al’ummomi Masu Karɓar Baƙuncin Dangote (DCCC) ne suka ɗauki nauyin tantancewa da zabar waɗanda za su amfana.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar da ta gabata an yi ta murna a cikin al’ummar Gboko a lokacin da kamfanin siminti na Dangote tare da wasu al’ummomi shida masu masaukin baƙi suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ci gaban al’umma mai cike da tarihi (CDA).

Ya ce, kamfanin zai sa ido kan yadda mata ‘yan kasuwa ke tafiya tare da tantance yadda ake zuba kuɗaɗen.

Da yake jawabi, muƙaddashin Daraktan Kamfanin Simintin Dangote, Injiniya Munusamy Murugan ya ce ƙarfafawar za ta kasance taron shekara-shekara.

Injiniya Murugan wanda Injiniya Taɓershima Soom ya wakilta ya ce sauran shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arzikin da aka jera sun haɗa da shirin manoma da shirin koyar da sana’o’i ga matasa da dai sauransu.

A nasa jawabin, shugaban sashin kula da ayyukan jin daɗin jama’a na kamfanin da ke Gboko, Johnson Kor, ya shaida wa wakilan al’ummar yankin cewa, kamfanin na yin ayyuka da yawa wajen tallafa wa al’ummar yankin, inda ya buƙace su da su kasance jakadu nagari na kamfanin simintin Dangote.

Da take mayar da martani, cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Ruth Ikyowe Tser, mai shekaru 37, ta ce za ta zuba kuɗin ne a cikin sana’arta ta noman rogo, yayin da ta yaba wa kamfanin bisa wannan tallafi.

Hakazalika, ɓishigh Comfort Msurshiona, mai shekaru 39, ta ce za ta yi amfani da kuɗin wajen bunƙasa kasuwancinta na sayar da kayayyaki.

By ukarofi