TCN ta sake gina hasumiyoyin lantarkin Kainji-Birnin Kebbi da suka faɗi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (TCN), ya ce ana ci gaba da aikin kafa hasumiyoyi guda uku a kan titin Kainji-Birnin Kebbi mai ƙarfin kilowatt 33Kɓ wanda ya ruguje a ranar 7 ga watan Mayu.

Babbar Manajan Kamfanin, Hulɗa da Jama’a, Ndidi Mbah, ne ta bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar a Abuja.

Ta bayyana cewa guguwar iska ce ta haddasa rugujewar hasumiyoyin da misalin ƙarfe 5:35 na yammacin ranar 7 ga Mayu.

Manajan ta ce, TCN ta haɗa wasu ‘yan kwangila guda uku zuwa wurin, waɗanda aka ba su aikin sake gina hasumiya ɗaya.

A cewarta, yunƙurin na da nufin hanzarta aiwatar da aikin maidowa da kuma rage raguwar wutar lantarki.

“A halin da ake ciki, an yi ƙoƙarin shawo kan matsalar taɓarɓarewar wutar lantarki ga Kaduna DisCo, wanda ke shafar wasu abokan hulɗar sa.

“A yanzu haka Sakkwato da Birnin Kebbi suna samun wutar lantarki tsakanin Megawatts shida zuwa bakwai (MW) daga tashar Mando ta layin Mando-Zaria-Funtua-Gusau-Talata-Mafara-Sokoto-Birnin Kebbi mai ƙarfin 132kɓ.

“TCN ta yaba da haƙuri da fahimtar al’ummomin da abin ya shafa, yayin da ‘yan kwangila ke aiki tuƙuru tare da injiniyoyi masu sa ido don sake gina hasumiya tare da sake shimfiɗa layin 330kɓ,” inji ta.

A halin da ake ciki, ta bayyana cewa kamfanin ya yi takaicin duk wata matsala da rugujewar ta haifar tare da ba da tabbacin aniyar kamfanin na maido da tsayayyen lantarki.

By ukarofi