Za mu haifar wa masu ɓoye shinkafa mummunar asara – BUA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Runkunin Kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirinsa na karya farashin shinkafa a Nijeriya, yana mai cewa nan gaba kaɗan waɗanda suka saye shinkafar suka ɓoye suna jira ta yi tsada, za su tafka mummunar asara.

ɗan kasuwar ya kuma bayyana cewa suna tattunawa da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan hanyoyin da za su bi domin ganin sun daidaita farashin siminti.

BUA ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa.

“Farashin kayan abinci na saukowa a Nijeriya kuma muna yin duk abin da za mu iya na ganin cewa mun mara wa gwamnati baya a kan hakan,” kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa, “Kun san shugaban ƙasa ya ɗage harajin shiga da kayan abinci kamar shinkafa da masara da alkama da dawa.

“A lokacin farashinsu ya tsahi sosai; a bara sai dai kuɗin buhun shinkafa ya kai N100,000, alkama da fulawa suka kai N80,000, masara ta kai N60,000, taliya kuma kwali ya kai N20,000.”

Ya bayyana cewa abin da ke faruaw shi ne, mutane ke saye shansherar shinkafa a lokacin kaka su ɓoye, daga baya su tsawwala farashin.

“Idan kaka ta wuce sai su ninka farashin. Wanna shi ne matsalar, kuma ba manoma ke cin moriyar ƙarin farshin ba, saboda tun da kaka sun riga sun sayar wa ’yan kasuwar da tan ɗaya a kan N400,000 ko N500,000.

“Su kuma waɗanda suka saye suka ɓoye, da zarar kaka ta wuce sai su ninka kuɗin ton zuwa N500,000,” inji BUA.

Ya bayyana cewa amma janye harajin shigo da abinci da gwamnati ta yi ya rikita lissafin masu ɓoye abincin, kuma a halin yanzu sun fara kokawa saboda irin asarar da suke tafkawa.

Ya ce, “duk da cewa ya kamata mu kare manomanmu, amma kuma yana da muhimmanci mu fahimci cewa yawan al’ummar ƙasar nan ya kai mutum miliyan 250, kuma yawancinsu ana sayar musu da kaya da tsadar da ta wuce misali, a sakamakon abin da wasu tsirarun kamfanoni ko mutane ke yi.

“Muna fata zuwa ƙarshen wannan shekara farashin shinkafa ba zai fi yadda yake a yanzu ba. Na tabbata da zarar lokaci ya yi manoma za su samu shinkafa a farashin da suka saba, kuma ba zai ƙaru ba a kasuwa, saboda mutane sun shirin masu ɓoye ta, kuma idan sun ɓoyen ma, asara suke yi,” inji ɗan kasuwan.

Game da tsadar siminit, BUA ya danganta matsalar a faɗuwar darajar naira a kan dala.

By ukarofi