Thierry Henry ya ba ‘yan Nijeriya haƙuri kan barƙwancin rashin sa’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren tsohon ɗan wasan ƙungiyar Arsenal, Thierry Henry ya yi ƙarin haske game da kalamansa akan Nijeriya yayin gasar Kofin Duniya na 2026 da ke gudana, yana mai cewa ba a fahimci tsokacinsa ba ne kuma ba da nufin cin fuska ya yi su ba akan ƙasar.

Tsohon ɗan wasan na Faransa ya bayyana haka ne yayin hira a shirin iShowSpeed gabanin wasan Amurka da Paraguay na rukunin D, wanda Amurkawa suka yi nasara da ci 4 da 1.

Henry ya yi barƙwancin ne a lokacin da aka ga ‘yan wasan Amurka sun shiga filin wasa sanye da rigunan ƙasarsu da safunan Nijeriya, inda ya bayyana hakan a matsayin “rashin sa’a”.

Wannan kalamai sun haifar da yamutsi a kafafen sada zumunta musamman acikin ‘yan Nijeriya, inda wasu ke ganin hakan a matsayin cin fuska ga ƙasar.

Saidai, tsohon ɗan wasan ya bayyana cewa abin da kalaman nasa suke nufi shi ne yadda tawagogin ƙasashe ke amfani da launin kaya daban-daban na shiga gasar Kofin Duniyar.

A cewarsa, yana matuƙar girmama Nijeriya da al’ummarta musamman saboda tarin magoya bayan Arsenal da suka fara son ƙungiyar saboda shi, yana mai cewa akwai buƙatar kada a yi masa mummunar fahimta.

By Babaji

Leave a Reply