Daga MAHDI MUS MAHAMMAD
TikTok ya cire bidiyo miliyan 2.4 na ’yan Nijeriya a cikin kwata na huɗu na 2024 saboda karya dokoki.
Kamfanin, wanda ByteDance ke tafiyar da shi, ya sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashe 50 da suka fi saka bidiyon karya doka a wannan lokacin.
Dangane da sabon rahoton TikTok na Tilasta Dokoki, jimlar bidiyo miliyan 153 ne aka saukar da su a duniya a ƙarshen 2024.
Rahoton ya bayyana cewa Amurka ce ta fi yawan waɗanda aka cire wa bidiyo, inda aka goge bidiyon miliyan 8.5.
Kamfanin ya bayyana cewa manyan kasuwanni 50 sun kai kusan kashi 90 na duk abubuwan da aka cire a cikin kwata.
Laifukan sun shafi nau’o’i da yawa, gami da mutunci da gaskiya, tsaro, lafiyar hankali da ɗabi’a, aminci, da wayewa.
Haka nan, TikTok ta cire asusu miliyan 211.5 a cikin lokacin, wanda ya ƙunshi asusun bogi da waɗanda ake zargi mallakar masu amfani ’yan ƙasa da shekaru 13.
Asusu na jabu ne ke da kaso mafi girma, tare da gogewa miliyan 185.3, yayin da aka yiwa alama asusu miliyan 20.5 don mallakar masu amfani da ƙananan shekaru.
An cire wasu asusu miliyan 5.6 saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.
A cikin wata sanarwa, TikTok ta jaddada ƙudurinta na kare dandamali daga ayyukan zamba.
“Muna ci gaba da taka-tsan-tsan a kokarinmu na gano barazanar daga waje da kuma kare dandalin daga asusun karya da hada kai.
“Waɗannan barazanar suna ci gaba da bincike da kai hari kan tsarinmu, wanda ke haifar da sauyi na lokaci-lokaci a cikin ma’auni da aka ruwaito.”
Kamfanin ya kuma lura cewa sabuntawa game da rarraba abubuwan so da mabiyan bogi a cikin ƙarshen shekara sun ba da gudunmawa ga wasu haɓakar abubuwan da aka gani na cirewa.
