Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatar da shirin samar da wutar lantarki a ɓangaren kiwon lafiya, da nufin magance ƙalubalen rashin wutar lantarki da ake fama da shi a cibiyoyin kula da lafiyar jama’a.
Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar a Abuja, ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Dr. Iziaƙ Salako, ya bayyana buƙatar gaggawa na samar da hanyoyin samar da wutar lantarki mai ɗorewa a asibitocin ƙasar nan.
Ya yi nuni da cewa ziyarar aiki da ya kai manyan cibiyoyin lafiya na tarayya ya nuna rashin wutar lantarki mai tsanani da tsadar lanatarki, wanda ke haifar da ƙalubale ga harkar kiwon lafiya.
“Kamar yadda ku ka sani, rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan ba su kasance masu gamsarwa ba game da samar da wutar lantarki a asibitocinmu na gwamnati, yayin da gwamnati ta ɓullo da tsare-tsare irin su tallafin wutar lantarki kashi 50 cikin 100 da kuma ƙananan na’urorin lantarki masu amfani da hasken rana a wasu asibitocin da aka zaɓa, wannan ƙoƙarin bai yi cikakken maganin matsalar ba, dole ne mu sake tunanin samar da wutar lantarki mai ɗorewa,” inji Salako.
Ya jaddada buƙatar samar da tsari na gwamnati baki ɗaya tare da ƙarfafa haɗin gwiwar jama’a da masu zaman kansu don jawo hankalin masu zuba jari a madadin hanyoyin samar da lantarki mai ɗorewa ga asibitoci.
Ya kuma amince da batutuwa kamar aukuwar gobara, satar muhimman ababen more rayuwa, da ƙalubalen kulawa a asibitocin a matsayin manyan hanyoyin da ke kawo cikas ga samar da lantarki.
Ya ƙara da cewa, “Lokacin gwaji da hanyoyin samar da lantarki da ba su dace ba ya wuce. Dole ne mu samar da dabaru masu hankali, haɗewar makamashi don rage kuɗaɗen wutar lantarki da asibitoci ke hauhawa, waɗanda ke shiga cikin ɗaruruwan miliyoyin Naira a kowane wata.”
Tattaunawar masu ruwa da tsaki na kasa kan samar da wutar lantarki a ɓangaren kiwon lafiya da za a gudanar a Abuja ko Legas, za a haɗa kan ƙwararru daga ɓangaren lafiya da wutar lantarki.
Kwamitin aiwatarwa yana da alhakin shirya tattaunawa, tabbatar da aiwatar da shawarwarinsa, da tattara albarkatu don ɗorewar wutar lantarki na wuraren kiwon lafiya.
Salako ya bayyana jin daɗinsa kan yadda ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, da ministan wutar lantarki, da hukumomin gwamnati, da kuma abokan ci gaba suka bayar da goyon bayansu wajen magance ƙalubalen wutar lantarki a fannin kiwon lafiya a Nijeriya.
