Tinubu na shirin saka harajin kashi biyar kan caca, wasanni da sadarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta gabatar da ƙudurin saka harajin kashi biyar cikin ɗari a kan ayyukan sadarwa, wasanni da caca a matsayin wani sabon ƙudiri na yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya.

Wannan shawara, wacce ke ƙunshe a cikin “Dokar Harajin Nijeriya,” na da nufin sanya harajin kan ayyuka daban-daban a faɗin ƙasar.

Kudirin mai taken; “ƙudirin dokar da zai daidai wasu dokoki kan haraji da kuma daidaita tsare-tsare na shari’a da suka shafi haraji da kuma kafa dokar harajin Nijeriya don samar da harajin kuɗaɗen shiga,” wanda aka samu daga Majalisar Dokoki a ranar 4 ga Oktoba, 2024.

Wani bincike kan dokar da aka gabatar a ranar Juma’a ya nuna cewa tana neman ɓullo da haraji kan ayyuka irin su wayar tarho, wasanni, caca da ake gudanarwa a Nijeriya.