LAFIYA UWAR JIKI: Illolin aikata istimina’i (masturbation) kashi na 4

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Illarsa ga al’aura:

Daukar tsawon lokaci ana aikata istimna’i na da haɗari ga al’aurar maza da ta mata. Bari mu fara da illolin da ke shafar al’ aurar maza. Mafi yawan mazan da su ka mayar da wannan aika-aika ɗabi’ar su na wayar gari da matsaloli kamar haka: 

1. Raunin mazakuta ta yadda namiji ba zai iya samun ƙarfin gamsar da mace ba. Yawan yin istimna’i shi ne ke gajiyar da hanyoyin jinin da ke kawo wa mazakuta jini. A ƙa’ ida, waɗannan hanyoyin jini su na shikawa ta yadda idan namiji ya shiga sha’awa, yawan jinin da ke shiga cikinsu zai ƙaru, hakan shi ne ke sa gaban ya miƙe. Yawan aikata istimna’i yana sa wa hanyoyin jinin su gaji ta yadda ba za su shika da kyau ba, domin isasshen jini ya kai ga mazakuta. A sakamakon haka, sai a samu raunin gaba.

2. Saurin inzali: fFitar maniyyi kafin lokacin da ya kamata a ce ya fita. Galibi idan namiji ya na aikata wannan abu, to manufarsa ita ce ya gamsar da kansa, ba ya tunanin gamsar da matarsa tunda shi kaɗai yake yi. Matsalar ita ce zai sabawar kansa kawowa da wuri domin kawai ya gamsar da kansa. Idan ya saba da hakan, to zai iya samun matsala ta saurin inzali yayin saduwa, wanda hakan naƙasu ne ga rayuwar aure, saboda zai gaza wajen gamsar da matarsa.

A na can a na ta muhawara akan cewa ko yawan istimna’i zai iya haifar da ciwon daji (ga wata gujiya da ke taimakawa wajen samar da ruwan maniyyi) ko kuwa ba zai haifar da ciwon daji ba! Ku tara a rubutu na gaba. 

Naku; Mustapha Ibrahim Abdullahi

©MIAbdullahi 2024