Daga UNCLE LARABI
Shin za mu iya jure wannan baƙar azabar mulkin zaluncin da shugabannin Nijeriya azzalumai ke yi mana? Zuwa wane lokacin tura za ta kai bango mu gaza jure wannan mugun baƙin zaluncin da suke yi mana?
A ranar Laraba (9-10-2024) kwatsam aka wayi gari da ƙarin kudin man fetur a NNPCL na ƙasa, wanda mallakin Gwamnatin Tarayya ne daga Naira 896 zuwa Naira 1030, wanda hakan ya ba wa sauran gidajen man na ɗaiɗaikun mutane ko kamfani damar ƙara nasu kuɗin man fetur ɗin, ƙila ma wasu su mayar da nasu zuwa Naira 1300.
Wannan ƙarin man fetur ɗin zai shafi ƙarin komai, kama tun daga ƙan abun hawa na haya har zuwa kayan masarufi. Hasbinallahu wa ni’imal wakil!!!
To, shin haka za mu zauna mu zuba Ido ana mana wannan mulkin zaluncin babu tausayi ko imani da talakawan da ake mulka a ƙasar?
Tun mu na ganin abun kamar raha, kamar wasa, yaƙin fa na neman ya cimma 60% na mutanen ƙasar, wanda idan ba a yi wasa ba zai cimma kusan 90 na mutanen ƙasar.
Yadda Naira ke ƙara lalacewa shi zai tabbatar maka da hakan wajen ruguza da yawan ’yan kasuwa za su dawo marasa jari. Masu jarin za su dawo kaɗan kuma babu wata riba mai yawa da za ta magance musu matsalolinsu, saboda hauhawar farashi na Dala ko fetur.
Talakawa da yawa abinci zai gagare su, duk da yanzu haka ma addin mutanen da ke kwana da yunwa da waɗanda suke rasa jarinsu ko sana’o’insu kullum ƙara ƙaruwa suke yi.
Zawarawa na sake yawaita sakamakon rashin iya ciyarwa da wasu mazan ke iyayi a wannan zamanin na mulkin Tinubu. Wasu kuma matan sun shiga fafutukar yadda za a taru a rufa wa juna asiri, a gudu tare a tsira tare. A dai samu a ce a na zaman zuren.
Ba sai na ɓata baki wajen faɗa muku cewar, kaso 75 na yawan haife-haife ya ragu ba. Duk wanda yake musu zai iya neman asibiti mafi kusa da shi ya je ya zauna a bakin ɗakin haihuwa zai ga a rana yanzu matan da ake karɓar haihuwarsu ba za su gaza cikin ‘yan yatsun Hannu ba, saɓanin da da har korar wasu ake a ce ba gado ko ba za a karɓe su ba. Yanzu haihuwar ta zama sai wane da wane.
To ina mafita?
Mafitar ita ce; mai zai hana tunda an gwada zanga-zanga an ga ba ta da riba, to mu gwada zaman gida ko da na kwana uku ne. Mu tsara ranakun a junanmu yadda kowa ba zai fito ba ya zauna a gida, don nuna ƙin amincewa da wannan mulkin zaluncin da ake yi mana a ƙasar nan. Na yi amanna gwamnati za ta fi jin ciwon hakan, domin za ta fi tafka mummunar asara a tsahon wannan kwana ukun da za mu yi na zaman gidan.
Na san wasu za su ce ai wani sai ya fita zai samu abinda zai ci. To, wanda ya ke da shi a kusa ko dafaffen abinci ne a girka a fito da shi waje, don taimaka wa wanda ba shi da shi ɗin. Mu daure mu jarraba wannan shawarar ko za mu samu mafita tunda ita dai ba fita bakin titi bare a samu wasu baragurbi su ɓata lamarin da sace-sace ko faɗa.
Abdullahi Jibril Dankantoma (UNCLE LARABI) marubuci ne kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Kano,
Laraba, 9-10-2024