Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi sabon Jami’in Kula da ƙorafe-ƙorafen Haraji na ƙasa, Mista John Nwabueze, a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani mataki da ke nuni da ƙudurin gwamnati na ƙara inganta gaskiya da ɗaukar alhaki a tsarin tattara haraji.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye a ɓangaren kuɗaɗen shiga, domin gyara tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati, rage tangal-tangal da samar da daidaitaccen yanayi ga ‘yan kasuwa da masu zuba jari.
Ofishin nai Kula da ƙorafe-ƙorafe na Haraji, wanda Gwamnatin Tarayya ta kafa kwanan nan, wani muhimmin ɓangare ne na ajandar gyaran tattalin arzikin shugaban ƙasa.
An tsara shi ne domin ƙarfafa gaskiya, inganta hanyoyin warware taƙaddama kan haraji, rage matsalar haraji mai maimaituwa, tare da kare ‘yan ƙasa da kamfanoni daga nauyin haraji ko tara da ba su dace ba.
A cewar Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, ofishin zai zama wata hanya mai cin gashin kanta da za ta karɓi koke-koke da suka shafi haraji, kuɗin kwastom da sauran cajin hukumomi. Wannan tsari na da nufin tabbatar da adalci a harkar haraji tare da ƙara amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.
A wajen taron, Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, sun halarta, lamarin da ya aara nuna muhimmancin sauyin da ake ƙoƙarin kafawa.
Mahukunta sun bayyana cewa wannan gyara zai ƙarfafa ɗaukar alhaki a ɓangaren gwamnati, ya ƙara wa masu zuba jari kwarin gwiwa, tare da bunƙasa gasa da ingancin tattalin arzikin Nijeriya a idon duniya. Sun kuma jaddada cewa kafa ofishin wata tubali ce mai ƙarfi da za ta taimaka wajen samar da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa da kwanciyar hankali.
Gwamnatin Tinubu ta sha nanata cewa gyaran hukumomi shi ne ginshiƙin farfaɗo da tattalin arziki, tare da ƙara kuɗaɗen shiga ba tare da ɗora wa jama’a nauyin da ba su iya ɗauka ba.
