Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙi karɓar baƙuncin tawaga ta musamman da Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aiko zuwa Nijeriya domin tattaunawa kan hare-haren ƙyamar baƙar fata da ake kai wa ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan Afirka a ƙasar.
Maimakon ganawa da tawagar, Shugaba Tinubu ya umarce ta da ta gana da ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda zai gabatar masa da rahoton tattaunawar.
Majiyoyi da dama daga Fadar Shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ministan Hulɗar ƙasashen Waje da Haɗin Gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ta isa Abuja tun ranar Juma’a domin neman ganawa da shugaban ƙasar.
Sai dai majiyoyin sun ce tawagar ta zo ba tare da sanar da Fadar Shugaban ƙasa a gaba ba. Bayan neman izinin ganawa, an fara sanar da su cewa za a iya ganin shugaban a ranar Litinin, amma daga bisani Tinubu ya umurce su da su gana da ƙaramin Ministan Harkokin Waje maimakon shi.
Wani jami’in Fadar Shugaban ƙasa ya ce shugaban bai saka wannan ganawa cikin jadawalinsa ba, yayin da wani jami’i ya tabbatar da cewa ba zai gana da tawagar ba.
Lamarin ya biyo bayan ƙaruwar takun saka tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu sakamakon sabbin hare-haren ƙiyayya da aka kai wa ‘yan Nijeriya da sauran baƙin haure a ƙasar, lamarin da ya tilasta kwashe ɗaruruwan ‘yan Nijeriya zuwa gida.
An kuma bayyana cewa Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, wadda ke wata ziyarar aiki a Addis Ababa, ta bayyana cewa bai dace shugaban ƙasa ya karɓi tawagar ba a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan Nijeriya da kasuwancinsu a Afirka ta Kudu.
Yayin da yake karɓar tawagar a Abuja, Ambasada Sola Enikanolaiye ya ce Shugaba Tinubu ne ya umarce shi da ya gana da su domin tattauna hanyoyin da za a kawo ƙarshen rikicin.
Ya bayyana cewa dangantakar Nijeriya da Afirka ta Kudu ta daɗe tana da ƙarfi, don haka bai kamata hare-haren ƙiyayya ga ‘yan Afirka su lalata wannan alaƙa ba.
Enikanolaiye ya ce hare-haren da ake kai wa ‘yan Nijeriya ba sabon abu ba ne, domin an samu makamantansu tun daga shekarun 1995, 1998, 2006, 2015, 2016, 2019, 2021, 2024 da kuma 2026.
Ya ƙara da cewa daga shekarar 2022 kaɗai, kimanin ‘yan Nijeriya 98 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da ya bayyana a matsayin Afrophobia, saboda galibin waɗanda abin ke shafa ‘yan Afirka ne, musamman ‘yan Nijeriya.
ƙaramin Ministan ya kuma tunatar da gwamnatin Afirka ta Kudu irin gudummawar da Nijeriya ta bayar wajen yaƙin kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata (Apartheid), yana mai cewa abin takaici ne a ce a yau ‘yan Nijeriya na fuskantar irin waɗannan hare-hare.
Ya jaddada cewa gwamnatin Nijeriya ba ta goyon bayan aikata laifi, amma duk wanda ake zargi da laifi ya kamata a bi hanyoyin shari’a wajen hukunta shi, maimakon ɗaukar doka a hannu.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu hare-haren suka faru a gaban jami’an tsaro ba tare da sun ɗauki mataki ba, yana mai cewa hakan na haifar da tambayoyi kan alhakin gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Enikanolaiye ya bayyana cewa hare-haren sun haddasa mummunan yanayin jin ƙai, inda aka kwashe kusan ‘yan Nijeriya 1,500 daga Afirka ta Kudu bayan sun rasa gidaje da dukiyoyinsu.
Da yake mayar da martani, shugaban tawagar Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ya ce Shugaba Ramaphosa ne ya aiko shi domin isar da saƙo ga Shugaba Tinubu tare da sake jaddada cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta goyon bayan ɗenophobia, wariyar launin fata ko wani nau’in ƙiyayya.
Sai dai ya ce gwamnatin ƙasarsa za ta ci gaba da aiwatar da dokokin shige da fice tare da yaƙi da aikata laifuka a cikin ƙasar.
Lamola ya ƙara da cewa matsalar ƙaura ta zama ƙalubale ga nahiyar Afirka baki ɗaya, saboda haka Nijeriya da Afirka ta Kudu na da alhakin yin aiki tare domin magance matsalar.
Ya bayyana fatan cewa tattaunawar da aka gudanar a Abuja za ta taimaka wajen rage zaman ɗar-ɗar tsakanin ƙasashen biyu tare da ƙarfafa dangantakar diflomasiyya.
An bayyana cewa ziyarar Lamola na daga cikin ƙoƙarin Shugaba Ramaphosa na rage tashin hankalin da ya biyo bayan hare-haren ɗenophobia, gabanin taron musamman na Tarayyar Afirka (AU) kan rigakafin rikice-rikice da warware su, wanda za a gudanar a Angola daga 29 zuwa 30 ga Agusta, 2026.
