Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sojojin Operation HAɗIN KAI (OPHK) sun daƙile yunƙurin da wasu ‘yan ta’addan ISWAP/JAS suka yi na kutsawa sansanin soji a Jihar Borno, tare da kwashe dalibai mata 21 zuwa wuri mai tsaro bayan samun sahihan bayanan sirri kan shirin kai hari.
Rahotannin ayyukan rundunar da aka fitar a ranar Litinin sun kuma tabbatar da kama wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane, wanda ke gudanar da ayyukansa tsakanin Nijeriya da Kamaru.
A cewar rahoton, sojojin Bataliya ta 3 da ke Forward Operating Base Logomani sun gano ta hanyar na’urar sa ido ta CCTɓ cewa ‘yan ta’addan ISWAP/JAS na kokarin kewaye sansaninsu. Nan take sojojin suka bude musu wuta, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa kafin su aiwatar da shirin kutsen.
A wani samame daban, sojojin Sector 3 sun samu bayanan sirri cewa wasu mutum bakwai da ake zargin ‘yan ISWAP/JAS ne dauke da bama-bamai na hannu sun bayyana a kusa da sansanin ‘yan gudun hijira na Water Board IDP Camp da ke Monguno.
Saboda haka, sojojin suka kwashe dalibai mata 21 daga masaukinsu zuwa Barikin Kinnasara domin kare lafiyarsu.
Rahoton ya ce ɗalibai uku sun kamu da farfadiya yayin kwashe su, amma an kai su asibiti inda aka ba su kulawar gaggawa, sannan aka kara tsaurara matakan tsaro a yankin.
A karamar hukumar Askira/Uba, sojojin 115 Task Force Battalion tare da mafarauta na gari sun fafata da ‘yan ta’adda a kauyen Surajo, inda maharan suka tsere suka bar kekuna uku da kwalayen sanyaya abubuwa guda biyu.
Hakazalika, sojojin 247 Reconnaissance Battalion tare da mafarauta sun kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane a Gaya, karamar hukumar Mubi South ta Jihar Adamawa.
Wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wata kungiyar masu garkuwa da mutane da ke da sansani a dajin Solere na kasar Kamaru, kuma suna shiga Nijeriya domin sace mutane.
A Jihar Kogi kuwa, sojojin Operation MESA tare da ‘yan sanda da jami’an tsaro na sa-kai sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi a kan hanyar Koton Karfe–Okparake, tare da kama mutum uku da ake zargi da ta’addanci.
An ƙwato bindigar hannu guda daya, babur daya, wayoyin hannu uku da kuma Naira 23,000 daga hannun wadanda ake zargin. Daga bisani an mika mutumin da aka ceto ga iyalansa.
A Jihar Kebbi kuma, sojojin Operation FANSAN YAMMA sun fatattaki wasu ‘yan ta’adda da suka kai hari a kan hanyar Wasagu–Ayu da ke karamar hukumar Wasagu, inda maharan suka tsere suka bar babura biyu a wurin.
