ICPC ta kai ƙarar likitan El-Rufai gaban Majalisar Likitoci kan zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta kai ƙarar likitan da ake zargi ya ƙirƙiri rahoton lafiya da aka yi amfani da shi wajen neman belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gaban Majalisar Likitoci da Likitocin Haƙora ta Nijeriya (MDCN), tana neman a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

A cikin wata takarda da ta aike wa Kwamitin Binciken Likitoci na MDCN, shugaban ICPC ya nemi a buɗe cikakken bincike kan Farfesa Bello Abubakar, babban ƙwararren likitan cutar daji (Clinical/Radiation Oncologist) da ke aiki a Asibitin ƙasa da ke Abuja.

Takardar, wadda Blueprint Manhaja ta gani, ta buƙaci kwamitin ya gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin cewa likitan ya aikata abin da ya saɓa wa ƙa’idojin aikin likita.

A cikin rantsuwar shaida da jami’in binciken ICPC, Aleɗ Omamuli, ya yi a gaban Babbar Kotun Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa El-Rufai ya gabatar da rahoton lafiya mai kwanan wata 10 ga Yunin 2026 domin neman beli saboda rashin lafiya.

Rahoton ya fito ne a kan takardar Asibitin ƙasa ta Abuja, kuma Farfesa Bello Abubakar ne ya sanya wa hannu, yana mai cewa ya dogara da bayanan lafiyar El-Rufai da ke asibitin.

Sai dai ICPC ta ce bayan ta nemi Asibitin ƙasa ya tabbatar da sahihancin rahoton, shugabannin asibitin sun bayyana cewa:

Ba a saka lambar marar lafiya a rahoton ba. Binciken bayanan marasa lafiya bai gano sunan El-Rufai ba. El-Rufai ba marar lafiya ba ne a asibitin. Babu tarihin gwaji, bincike ko dubawar likita da ta dace da abin da rahoton ya ƙunsa.

Sannan hukumar asibitin ba ta san da fitar da rahoton ba, kuma ba ta ba da izinin amfani da takardarta ba.

Asibitin ya kuma tabbatar wa ICPC cewa Bello Abubakar tsohon ma’aikacinsa ne da yanzu yake aiki a ƙarƙashin kwangila.

“Ba a yi cikakken binciken lafiya ba”

ICPC ta ce tun bayan kama El-Rufai a watan Fabrairun 2026, ana ci gaba da duba lafiyarsa tare da halartar likitocinsa.

A cewar hukumar, Bello Abubakar ya ziyarci El-Rufai sau biyu kacal, a ranakun 8 da 18 ga Yunin 2026, inda aka auna masa hawan jini kawai, ba tare da wani gwaji, ɗaukar jini, fitsari ko wasu binciken likitanci ba.

Har ila yau, ICPC ta ce likitocin El-Rufai da na hukumar ba su taɓa gano alamomin cutar da rahoton ya ambata ba.

Saboda haka, hukumar ta zargi Bello Abubakar da fitar da rahoton lafiya da ra’ayin ƙwararru ba tare da hujjojin binciken lafiya, gwaje-gwaje ko bayanan asibiti ba, tare da amfani da takardar Asibitin ƙasa ba tare da izininsa ba.

A baya dai ICPC ta gurfanar da Bello Abubakar a gaban kotu kan tuhume-tuɗume huɗu, ciki har da: Bayar da bayanan ƙarya ga jami’in gwamnati; amfani da matsayinsa wajen ba da wata fa’ida ba bisa ƙa’ida ba; haɗa baki wajen ƙirƙirar bayanan ƙarya; da kuma gabatar da rahoton da ake zargin na bogi kamar yana da amincewar Asibitin ƙasa.

Ana kuma sa ran Babban Daraktan Asibitin ƙasa, Muhammad Mahmud, zai ba kotu shaida cewa an fitar da rahoton ba tare da cikakken binciken lafiya ba, kuma asibitin bai amince da shi ba.

Bello Abubakar na hannun ICPC a halin yanzu, kuma ba a samu jin ta bakinsa kan zarge-zargen ba.

A gefe guda, Nasir El-Rufai na fuskantar shari’o’in cin hanci da rashawa da dama da ICPC ta shigar a kansa. Ya musanta dukkan zarge-zargen, ya roƙi kotu da cewa ba shi da laifi, sannan ya zargi gwamnatin tarayya da ta Jihar Kaduna da amfani da shari’o’in wajen ci gaba da tsare shi.

A bisa doka, Bello Abubakar da Nasir El-Rufai ana ɗaukarsu marasa laifi har sai kotu ta same su da laifi.

By ukarofi