Mahara sun kashe mutum 30, ciki har da yara biyar ’yan gida ɗaya a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu, ciki har da ƙananan yara biyar ’yan gida ɗaya, bayan wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai mummunan hari ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru Chawai, a ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Litinin, inda maharan suka farmaki ƙauyen, suka kashe mutane da dama, suka jikkata wasu tare da ƙona gidaje masu yawa.

Rahotanni sun bayyana cewa yara biyar ɗin, waɗanda dukkansu ’ya’yan wani magidanci mai suna Emmanuel ne, sun rasa rayukansu yayin da iyayensu suka tsallake rijiya da baya bayan sun tsere daga ƙauyen lokacin harin. Da suka dawo, sai suka tarar an kashe dukkan ’ya’yansu biyar.

Tsohon shugaban matasan yankin, Kwamared Friday Ango, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin ya fara ne da misalin ƙarfe 12:35 na dare.

Ya ce, “Mutum 24 ne aka tabbatar sun mutu a lokacin da na samu bayanai, amma mai yiwuwa adadin ya ƙaru daga baya.”

Ango ya ƙara da cewa babu rahoton sace mutane a harin, yana mai bayyana cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da mata, yara da kuma tsofaffi.

Ya bayyana sunayen yaran da suka mutu da suka haɗa da Deborah Emmanuel, Friday Emmanuel, Yusuf Emmanuel, Yunana Emmanuel da Irimiya Emmanuel.

A cewarsa, mutane da dama sun kuma samu raunuka, duk da cewa ba a tantance adadinsu ba.

Ya ce maharan sun shiga ƙauyen da manyan makamai, abin da ya sa mazauna yankin suka kasa kare kansu.

“Mutane sun rika guduwa domin tsira da rayukansu, yayin da waɗanda ba su samu damar tserewa ba aka kashe su,” inji shi.

Ango ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin ne bayan maharan sun riga sun tsere.

Ya kuma musanta rahotannin da ke cewa rikicin makiyaya da manoma ne ya haddasa harin, yana mai cewa an kai wa mutanen Naridon hari ne ba tare da wata tsokana ba.

A cewarsa, al’ummomin ƙaramar Hukumar Kauru sun daɗe suna fuskantar hare-hare iri ɗaya, kuma suna buƙatar ƙarin kariya daga hukumomin tsaro.

Hotunan da aka samu daga yankin sun nuna gidaje da aka ƙone, dukiyoyin da suka lalace da kuma gawarwakin waɗanda aka kashe, yayin da wani bidiyo ya nuna mata da yara suna makoki kafin gudanar da jana’izar mamatan.

Shi ma tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Kauru, Musa Waziri, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa yankin ya daɗe yana fama da rikice-rikice saboda kusancinsa da Jihar Filato.

Sai dai ya yi gargadin cewa bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci kan musabbabin harin ba, domin irin waɗannan hare-hare na iya kasancewa sakamakon rikice-rikicen da ke bazuwa daga yankunan maƙwabta.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Al’ummar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta yi Allah-wadai da harin, tare da yin kira ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna da ta ɗauki matakan gaggawa domin dakƙle taɓarɓarewar tsaro a yankin.

ƙungiyar ta buƙaci a tura ƙarin jami’an tsaro, musamman na kwantar da tarzoma da na yaƙi da ta’addanci, zuwa ƙananan hukumomin Kajuru, Chikun, Kauru da Zangon Kataf, tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri da yawaita sintiri.

Wani masanin harkokin tsaro, Mohammed Ali, ya kuma shawarci gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari wajen tattara bayanan sirri domin dakile hare-haren ’yan bindiga, satar mutane da satar shanu a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

A halin da ake ciki, ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar PDP, Hon. Usman Shehu Bawa (ABG), ya bayyana harin a matsayin dabbanci da ke buƙatar matakan gaggawa daga gwamnati da hukumomin tsaro.

Ya buƙaci a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa ƙaramar Hukumar Kauru da sauran yankunan da ke cikin haɗari domin hana sake afkuwar irin wannan hari.

Hakazalika, Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa ta karɓi labarin cikin alhini da takaici.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar, gwamnatin ta ce ta umarci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen kamo waɗanda suka aikata harin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Uba Sani ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansu, Ya bai wa waɗanda suka ji rauni lafiya, sannan ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) da ta kai tallafin gaggawa ga iyalan da abin ya shafa.

Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da haɗa kai da gwamnatin Jihar Filato, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsaro da dawo da zaman lafiya a yankunan kan iyakar jihohin Kaduna da Filato.

By ukarofi

Leave a Reply