An ƙaddamar da ba da takardar aikin dindin ta malaman makaranta, sama da mutum 130 ƙarƙashin sahalewar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a ƙaramar hukumar Bichi, wadda ta kasance a cikin ƙananan hukumomi 44 da suka rabauta a faɗin jihar Kano.
Kamar yadda jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta sanar.
Shugaban majalisar yankin, Alhaji Hamza Sule Maifata, a yayin gudanar da gangamin taron a sakatariyar ƙaramar hukumar, ya buƙaci waɗanda suka rabauta da aikin koyarwar, su zama jajirtattu masu amana wajen zuwa aiki koda yaushe kuma da yin aikin tuƙuru a kan lokaci, domin sauke haƙƙin da ya rataya a wuyansu domin cika muradun Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina al’umma a jihar.
“Idan ba za ka iya ba ko ba ka da sha’awa; kada ka wahalar da kanka ka wahalar da mu, domin ko zuwa mu canjo ofa ma ka wahalar da mu, zahiri idan ba ka zuwa ba za mu sa ma ido mu ƙyale ka ba; wata yana ƙarewa idan ka matsa wayarka kana zaton caji ne ya ƙare ba za ka ga albashi ba, waɗanda suka mai da hankali suke zuwa aiki tare da yin aikin kaɗai za mu riƙa biyansu albashi” Alhaji Hamza Sule Maifata.
A nasa ɓangaren sakataren kwamitin ilimi, na ɗan majalisar tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, Malam Ali Abdullahi Habib, bayan yaba wa Gwamnatin jiha da jagororin yankin da ma ƙasa baki ɗaya, ya bayyana ɗan majalisar ba shi da burin da ya wuce samar da ingantaccen ilimi a ƙaramar hukumar bisa la’akari da irin yadda yake ɗawainiya da harkokin ilimi a sassan yankin.
“Duba da cewa mai girma Gwamna ya ɗebi sababbin amare na malaman makaranta, bisa haka domin su samu nutsuwar koyo da koyarwa ta hanyar samar musu da yanayi mai kyau, ɗan majalisar tarayya ya kafa kwamitin kar-ta-kwana domin su tabbatar sun gyara makarantun firamare guda 76 dake ƙaramar hukumar Bichi na ɓangaren hukumar ilimin bai-ɗaya na yankin.” Malam Ali Abdullahi Habib.
Da yake jawabi sakataren ilimi na yankin, Malam Bashir Ishaq Muhammad, ya ce ba za su ci amanar ƙasa da jiha da ƙaramar hukumarsu ba, don haka ya ja hankalin waɗanda aka bai wa aikin kan cewar Allah ne ya zaɓe su ta hanyar jajircewar jagororin yankin, domin tabbatar da ‘ya’yan jikokinsu sun amfana da abin da za su bari a nan gaba.
“Ya kamata ku sa ran cewa wannan aikin zai iya kai mutum har aljannah, domin ba abin da muka sani illa koyarwa da ba mu tsaya mun koyar yadda yakamata ba, da ba mu zo inda muke ba da kuma ban tsaya a nan gurin ba! ” Malam Bashir Ishaq Muhammad.
A wani cigaba, Malama Asma’u Jume Ahmad shugabar ƙungiyar mata da ke hukumar Ilimin yankin a sashen wayar da kan al’umma, ta bayyana irin yadda suke ɗaukar nauyin koya wa yara sana’o’i daga bakin firamare, domin farfaɗo da tattalin arziki tun daga tushe.
“Akwai daga cikin sana’o’i 31 da muke buƙatar tallafi, idan aka samar mana kayan aiki za a ƙarfafe mu, domin Bichi tana da girma muna so mu shiga har cikin ƙauyuka.
A hannu guda ɓangaren da suka amfana da takardar aiki, Malama Hadiza Isyaku Ibrahim, ta bayyana jin daɗinsu tare da cewa ayyukan alheri irin wannan ba sabon abu ba ne ga Shugaban ƙaramar hukumar Alhaji Hamza Sule Maifata; dama can aikin shi ne samar da ayyukan yi ga jama’a.
“Saboda haka muna masa godiya, Allah ya saka da alheri ya ƙara masa ɗaukaka ya sa ya fi haka.” Malama Hadiza Isyaku Ibrahim.
