
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na daina biyan kuɗaɗen tallafi a fannin wutar lantarkin Nijeriya, wanda za a fara daga shekarar 2027.
Ministan Lantarki Joseph Tegbe ne ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a ranar Juma’a, yayin da yake warware matsalolin da suka shafi bashi a fannin lantarkin ƙasar.
Ya bayyana cewa, za a cire tallafin da kaɗan da kaɗan, yana mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a gudanar da al’amarin cikin tsari domi tabbatar da cewa sun amfana da tsarin.
Minutes ya kuma jaddada aniyar gwamnatin tarayyar ta babu shirin ƙara kuɗin lantarki da al’umma ke biya duk da ƙoƙarinta na cire tallafin fannin.
Ya ƙara da cewa, duk da matakin daina biyan kuɗaɗen tallafin daga 2027, gwamnatin za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen ba wa kwastomomin lantarki kariya yayin da ta aiwatar da sauyin.
Wannan mataki na nufin gwamnatin ta soke cire tallafin har sai a shekarar 2027.
