
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da gaggauta soke Kwamitin Aiwatarwa na Shugaban ƙasa (PIC) akan harkokin gudanar da kadarorin Gwamnatin Tarayya.
Tinubu ya ce, dukkan wasu al’amura da suka shafi kwamitin daga yanzu, za su koma ƙarƙashin kulawar Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN).
A ranar 22 ga watan Maris, 2001 ne Majalisar Zartarwar ta amince da samar da kwamitin tuntuɓa domin samar da farar takardar da za ta taimaka wajen aiwatar da shawarwarinta akan al’amarin. Kwamitin ya yi aiki har na tsawon watanni 21 kana ya miƙa rahotonsa.
A sanarwar da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a dogon nazari, gwamnatin ta ce ta lura cewa PIC tana aiki hatta a sama da ainihin huruminta, lamarin da ya janyo shari’o’i a sassan Nijeriya don haka babu amfanin ta cigaba da wanzuwa.
Ya bayyana cewa, gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne tare bai wa antonin ragamar jagorancin ayyukan da aka ɗora wa kwamitin, wanda ya fara aiki tun a ranar 25 ga Nuwamba, 2025.
Baya ga haka, an kuma umarci B. S. Dutsin-Ma wanda ya mata aikin sakatare, da ya janye aiki a muƙamin a matsayin mai wakiltar kwamitin da gwamnatin tarayya kan harkokin.
A shekarar 2000 ne aka kafa PIC a zamanin tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da nufin ya sanya ido kan mallaka, sayarwa da bayar da hayar kadarorin gwamnatin tarayyar a ƙarƙashin tsare-tsaren kuɗaɗen gwamnati.
