
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ce kwanan nan za ta fitar da cikakken bayani akan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur da kuma gyaran tsare-tsaren canjin kuɗi, domin amsa tambayoyin da jama’a ke yi kan inda kuɗaɗen suka je.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin ta kuma ce an tafiyar da kuɗaɗen tallafin da na gyaran tsare-tsaren canjin kuɗi ne ta hanyar warware basusukan gudanarwa da ƙarin adadin kashe-kashen gwamnati, yayin da jami’an gwamnati ke cigaba da bayar da kariya ga gyare-gyaren wajen danganta su da tsadar rayuwa.
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron Ƙungiyar Kasuwannin Afrika Masu Tasowa da aka gudanar a Abuja.
A cewarsa, tambayar da ake yi akan kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin mai da canjin kuɗi tambaya ce mai muhimmanci, yana mai cewa gwamnati za ta wallafa cikakken bayanin yadda aka kashe su cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya bayyana cewa, wani ɓangare na kuɗaɗen ya tafi wajen biyan bashin gwamnati, aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000, da kuma shirye-shiryen tallafi irin su Asusun Bayar da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), wanda ya ce ya tallafa wa fiye da ɗalibai miliyan 1.5.
Haka kuma, ministan ya yi watsi da iƙirarin Asusun Ƙasa-da-ƙasa (IMF) na cewa har yanzu miliyoyin ‘yan Nijeriya na fama da talauci duk da gyare-gyaren da masu ruba jari suka yi maraba da su a ƙasar, yana mai cewa rashin samun ainihin wadatar kuɗaɗe akai-akai abu ne da ba a iya kauce masa na ƙalubale da zai cire tallafi na tsawon lokaci da kuma aiwatar da gyare-gyaren canjin kuɗin waje.
