Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar haɗin kan mawaƙan bege (Coalition of Shu’ara Katsina State) ta Jihar Katsina ta kai ziyarar sada zumunci ga shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus-Sunnah).
Da yake gabatar da jawabin dalilin ziyarar, shugaban ƙungiyar haɗin kan mawaƙan bege a Katsina, Sayyadi Abubakar Ɗan Masani, ya bayyana cewa an kawo wannan ziyarar ne domin ƙarfafa zumunci da kuma gabatar da ƙungiyar da manufofinta, tare da neman shawarwari.
A nasa jawabin, Sheikh Yakubu Musa ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara da shugabannin ƙungiyar suka kawo masa.
Ya bayyana cewa samuwar ƙungiyar na da matuƙar muhimmanci wajen tsabtace da inganta waƙoƙin bege, domin kauce wa wuce gona da iri da wasu ke yi, tare da tabbatar da cewa waƙoƙin sun kasance cikin tsarin da ya dace da koyarwar Musulunci.
Ya kuma gabatar da tafsirin ayoyi na 224 zuwa 227 na Suratul Shu’ara, inda ya yi kira ga mawaƙan da su kasance cikin waɗanda Allah Ya ambata da yabo a ƙarshen ayoyin, waɗanda suka haɗa da masu imani, aikata kyawawan ayyuka da yawan ambaton Allah.
Ya ƙara da yin kira ga mambobin ƙungiyar da su yi amfani da baiwar da Allah ya ba su wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma, da shiryar da mutane zuwa ga alheri, tare da tabbatar da cewa waƙoƙin bege sun zama hanyar isar da saƙon alheri da kyawawan ɗabi’u.
A ƙarshe, Sheikh Yakubu Musa ya yi addu’ar Allah ya taimaki ƙungiyar wajen cimma manufofinta, ya sanya ayyukanta su zama sanadin alheri da shiryar da al’umma, ya kuma sanya su cikin “kaɗan ɗin da Allah ya yi magana da su da yabo” a cikin ayoyin Suratul Shu’ara.
