Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta sanar da haramta wasu al’adu da ayyukan da ake gudanarwa yayin bukukuwa da shirye-shiryen aure, tana mai cewa sun saɓa wa koyarwar Musulunci da kyawawan ɗabi’u.
Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka haramta akwai kayan “Na Gani Ina So” (See I Loɓe), wato al’adar da saurayi ke kai wa iyayen budurwa kayan sha, biskit, alewa, goro da sauran kyaututtuka a lokacin neman aure.
Hukumar ta kuma haramta gudanar da sana’ar DJ da kunna waƙoƙin Wazigidi a bukukuwa da tarukan nishaɗi da maza da mata ke cakuɗuwa.
Haka kuma, Hisbah ta hana amfani da manyan lasifika a kan baburan Keke NAPEP, tare da haramta zaman mata a gefen direban Keke NAPEP.
Bugu da ƙari, hukumar ta haramta wasu salon aski da ta bayyana a matsayin na rashin tarbiyya ga yara da matasa, tare da yin kira ga jama’a su rage tsaurara sharuɗɗan lefe domin kauce wa almubazzaranci da basussuka.
Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato, Malam Usman Abdullahi Jatau, ya ce dokar ta fara aiki nan take. Ya bayyana cewa manufar matakin ita ce kare kyawawan ɗabi’u da tabbatar da cewa ana gudanar da aure bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Ya gargaɗi masu shirya bukukuwa, masu sana’ar DJ da sauran masu ruwa da tsaki da su bi sabbin ƙa’idojin, yana mai cewa hukumar za ta ɗauki matakin doka kan duk wanda ya karya su.
Jatau ya kuma buƙaci iyaye da masu shirin yin aure da su sauƙaƙa lefe tare da guje wa almubazzaranci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin da ke tasowa sakamakon tsadar shirye-shiryen aure.
