Tinubu ya dawo da Shugaban NTA kan muƙaminsa mako guda da sauke shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci a dawo da Salihu Abdullahi Demos kan muƙamin darakta-janar na gidan talabijin na NTA a yau Talata.

Dembos ya bar muƙamin ne a kwanan nan bayan wasu ƴan gyare-gyare da aka yi wa hukumar gudanarwar gidan talabijin ɗin.

A watan Oktoban 2023 Shugaba Tinubu ya naɗa Dembos a muƙamin, inda a yanzu zai dawo domin kammala wa’adinsa na shekara uku.

Kamar haka ne Shugaban Ƙasar ya umarci a dawo da Ayo Adewuyi, wato daraktan yaɗa labarai kan muƙaminsa domin cika zangonsa na shekara uku, wanda zai ƙare a 2027.

Hakan na nufin an rushe naɗin tawagar jagororin gidan talabijin ɗin da gwamnati ta yi a makon da ya gabata.

By Babaji