Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) da Bankin Duniya ke ɗaukar nauyi zai gina sabbin makarantu 26 tare da gyara wasu 537 a faɗin Jihar Gombe, wanda ya kai jimillar makarantu 563.
Daga cikin wannan adadi, ƙaramar hukumar Gombe ita ce za ta fi amfana, inda za a gyara makarantu 45 da kuma gina sabbi guda uku a unguwannin Buhari Estate, Pilot Annex da Malam Inna. Haka kuma akwai ƙarin ayyuka da za’a gudanar a makarantar Orji da Model.
Shugabar shirin AGILE a jihar, Dakta Amina Haruna Abdul, ta bayyana hakan yayin da ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, domin gabatar da tsarin kula da muhalli da zamantakewa (ESMP) na aikin.
Ta samu wakilcin jami’in kula da muhalli na shirin, Jabiru Saleh Kilawa.
Ta ce an zaɓi makarantun da za a yi wa aikin bisa sharuɗɗan bankin duniya da suka haɗa da kasancewar akwai isasshen fili a makarantar, yawan ɗalibai da kuma kasancewar makarantar ta kai kilomita biyu tsakanin ta da wata.
A nasa jawabin, Barista Haruna wanda kuma shi ne shugaban ALGON a jihar, ya gode wa AGILE bisa yadda shirin zai ƙarfafa ƙoƙarin gwamnati wajen inganta ilimi.
Ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya da ya tabbatar da shigar jihar cikin shirin, yana mai cewa wannan dama ta zo a kan kari musamman ga ƙaramar hukumar sa ta Gombe wadda tafi kowacce yawan jama’a a jihar.
Shugaban ƙaramar hukumar nan take ya kafa kwamitin da sakatare na ilimi zai jagoranta tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya domin sa ido kan aiwatar da aikin yadda ya kamata.
