Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi ya ce aƙalla ayyuka 2,000 da ba a kammala ba gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gada, waɗanda ke zuƙar Tiriliyoyin nairori daga asusun ƙasa.
Ministan ya ce Ma’aikatarsu ba ta shakkar ɗaukar manyan matakan inda a halin yanzu an soke kwangiloli goma na wasu kamfanoni.
Mista Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani zama da masu-ruwa-da-tsaki Jihar Ondo kan haɗe wani ɓangare na babbar hanya mai tsawon kilomita 63 ta Legas zuwa Calabar.
Ya ce, samun Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaba, kyauta ce ga al’ummar Nijeriya, ya na mai bayyana wasu ayyuka da za su ɗauki dogon zango ana morar su.
Ya kuma ce titin zai ratsa jihohi bakwai ne wanda kuma hakan zai bada damar samar da sana’o’i da dama acikin al’umma.
Ya tabbatar da cewa za a kammala tsara ɓangaren titin da ke Ondo a watan Nuwamba.
Gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ya yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya ke tuna jihar yayin da ya tashi yin ayyukan ci-gaba.