Ya kamata manema labarai su fahimci shirin Tinubu ga Nijeriya – Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati da gidajen jaridu ba abokanan hamayya bane face takwarori ga harkokin gina ƙasa.

Ministan ya faɗi haka ne a lokacin da hukumar gudanarwa ta jaridar Guardian ta kai masa ziyara ofishinsa a ranar Alhamis.

Ya ce, samar da ci-gaba wa ƙasa aiki ne na kama-kama tsakanin ɓangarori, ya na mai cewa a matsayin ƴan jarida na masu lura da lamuran al’umma, akwai buƙatar su ƙara ƙaimi wajen kare martabar demokraɗiyyar Nijeriya da tabbatar da haɗin-kai da zaman lafiya acikin al’umma waɗanda za su su taimaka wajen samun riba wa ƙasar.

Ya kuma yaba wa jaridar kan ƙoƙarinta na tabbatar da demokraɗiyyar Nijeriya tare da yaƙar tsarin mulkin soji inda ya yi kira gare ta da ta cigaba da goyon bayan tsarin mulkin ƙasar don kai al’umma ga nasarori a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yi wa Nijeriya gyare-gyare masu amfani.