An tashi a zaman Gwamnatin Tarayya da ma’aikatan jami’o’i ba a cimma matsaya ba

Daga BELLO A. BABAJI

Zaman da aka gudanar tsakanin Gwamnatin Tarayya da kwamitin haɗaka na ƙungiyoyin jami’o’i (NASU da SSANU) a ranar Alhamis ya ƙare ba tare an cimma matsaya ba.

Tsohon Ƙaramin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu ya jagoranci zaman a Ma’aikatar Ilimi wanda an shirya shi ne don tattauna batun yajin aikin da ƙungiyoyin ke yi.

Babban Sakataren Ma’aikatar, Nasir Gwarzo na daga cikin wanɗanda suka halarci zaman.

A ranar Litinin ne ƙungiyoyin suka shiga yajin aiki mara iyaka sakamakon albashinsu na watanni huɗu da aka riƙe, wanda a saboda haka ne harkokin jami’o’i suka ja baya a Nijeriya.

A yayin hira da Shugaban SSANU na Ƙasa, Mohammed Ibrahim, ya bayyana cewa manya ma’aikata da suka haɗa da mataimakan shugabannin jami’o’i, bososhi da rijistirori ba su samu albashi na tsawon wata huɗu ba.

Don haka ne ya ce jami’o’i za su cigaba da zama a rufe har sai an biya su kuɗaɗensu.

Wani jami’i a zaman ya ce tabbas za a biya kuɗin amma wannan ba shi ne na farko ba da ake faɗan irin haka, ya na mai cewa hakan ba zai sa a janye yajin aikin ba.

Kawo yanzu dai gwamnati ba ta bayyana lokacin da za a biya kuɗaɗen ba, inda tuni suka sanar da ita cewa ba za su koma ba har sai an biya su, kamar yadda mataimakin SSANU, Abdussobur Salaam ya bayyana.