Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da naɗa Ruben Amorim a matsayin sabon mai horar da ƴan wasanta maza gabannin kammala cike ƙa’idar shiga ƙasa.
Manchester United ta bayyana haka ne ta kafofinta na sada zumunta a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, 2024.
Ta ce, zai kasance tare da ita har zuwa watan Yunin 2027 da zaɓin tsawaita zamansa na shekara ɗaya.
Da zarar ya kammala sauke nauyin da ke kansa na ƙungiyar da ya ke wa aiki a yanzu, zai je Manchester United a ranar 11 ga watan Nuwamba.