Tinubu ya kori Mataimaki na Musamman kan harkokin tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fadar Shugaban ƙasa a ranar Litinin, 8 ga Satumba 2025, ta bayyana cewa, an kori Mista Fegho John Umunubo daga matsayin Mai Taimakawa Shugaban ƙasa na Musamman kan Harkokin Tattalin Arzikin Dijital da ƙirƙire-ƙirƙire a Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa.

Sanarwar, wacce Abiodun Oladunjoye, Daraktan Hulɗa da Jama’a a Fadar Shugaban ƙasa ya sanya hannu a kai, ta bayyana cewa, korar Umunubo ta fara aiki nan take, kuma daga yanzu ba ya riƙe da kowanne matsayi ko wakiltar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kowane mataki.

A cikin sanarwar an yi ƙarin gargaɗi ga al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire a gida da waje da kada su yi hulɗa da Umunubo da sunan gwamnati. Fadar Shugaban ƙasa ta nuna cewa, duk wanda ya ci gaba da hulɗa da shi a matsayin jami’in gwamnati zai yi hakan ne a hatsarin kansa.

Sai dai duk da cewa ba a bayyana ainihin dalilin korar ba, masana sun ce wannan mataki na cikin jerin sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke yi domin daidaita muƙamai da kuma tsara sabuwar dabara ta shugabanci.

Wani masani kan harkar tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire daga Jami’ar Legas ya bayyana cewa: “Sauye-sauyen gwamnati wani abu ne da ake sa ran gani, musamman idan shugaban ƙasa na son ganin tsari ya dace da manufofin sa. Amma abu mai muhimmanci shi ne, a tabbatar da cewa wannan ɓangare na ƙirƙire-ƙirƙire bai yi ƙasa a gwiwa ba.”

Masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire sun nuna damuwa da korar, musamman ganin cewa wannan ɓangare na ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin zamani da ke kawo kuɗaɗen shiga ga matasa da ‘yan kasuwa.

Wasu masana sun ce akwai buƙatar gwamnatin Tinubu ta sanya sabon jami’in da zai fahimci irin ƙalubalen da ke fannin, kamar rashin tsayayyen tsarin kariya ga masu ƙirƙira, matsalar zamba a intanet, da kuma ƙarancin jarin gwamnati a masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire.

Ana sa ran cewa nan ba da jimawa ba za a bayyana wanda zai gaji kujerar Umunubo, domin gwamnati ta ce, tana ci gaba da tsara sabbin matakan da za su haɓaka tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire da dijital, musamman ga matasa da ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

By ukarofi