Babban Daraktan KSMC ya ziyarci Qausain TV tare da neman haɗin gwiwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon Daraktan Gudanarwa na Kaduna State Media Corporation (KSMC), Hon. Ben Kure, ya kai ziyarar ban girma zuwa hedikwatar Qausain TV dake Kaduna.

A yayin ziyarar, Malam Kure ya yaba wa Qausain TV bisa ƙirƙira da jajircewa wajen ingantaccen yaɗa shirye-shirye. Ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin gidajen yaɗa labarai yana da matuƙar muhimmanci domin ci gaban shirye-shirye, faɗaɗa isarwa da kuma samar da labarai masu tasiri.

Shugaban Qausain TV Nasir Musa Idris (Albani Agege) ya bayyana wannan ziyara a matsayin ta dace kuma mai muhimmanci, tare da tabbatar da cikakken shiri na yin haɗin gwiwa da KSMC a fannonin raba shirye-shirye, gina ƙwarewa, horaswa, da kuma shirye-shiryen haɗaka.

ɓangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da ainihin fannonin haɗin gwiwa da zai amfanar da juna da ƙasa baki ɗaya.

Hakazalika a gabanin ziyarar ce hukumar gudanarwar Qausain TV ta sanar da naɗin Injiniya AbdurRahman Hassan a matsayin sabon Janar Manaja.

Injiniya Hassan, ƙwararre ne wanda ya kwashe shekaru da dama a harkar yaɗa labarai, inda ya yi ritaya a matsayin Mataimakin Darakta a Gidan Rediyon Nijeriya Kaduna. A tsawon lokacin da ya yi a harkar, ya riƙe muƙamai da dama a kamfanin, ciki har da shugaban sashen Injiniyanci, shugaban ayyuka, sannan ya riƙe muƙamin shugaban gidan rediyon Nigeria Investment Limited.

By ukarofi