Tinubu ya naɗa ɗan IBB, Muhammad shugaban Bankin Noma da wasu jami’ai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin sabon shugaban Bankin Noma da aka sabunta wa tsari.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya faɗi hakan a wata takarda, ranar Alhamis.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa wasu mutane guda bakwai da za su yi aiki a matsayin shugabanni da daraktocin wasu hukumomin gwamnati.

Muhammad Babangida mai shekaru 53 ya yi digirinsa na farko ne akan harkar kasuwanci, sannan ya yi na biyu a tsangayar hulɗa da jama’a da sadarwar kasuwanci a Jami’ar ‘European University of Montreux’ dake ƙasar Switzerland.

Ya kuma kammala karatu akan Gwamnatin Haɗaka a makaratun Havard Business School a shekarar 2002.

Naɗin muƙaman wani ɓangare ne na ƙoƙarin Shugaba Tinubu wajen ganin an samar da daidaiton shiyyoyi a raba muƙamai da yi wa al’umma hidima.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da;

“Lydia Kalat Musa (Kaduna State): Chairman, Oil and Gas Free Zone Authority (OGFZA); Jamilu Wada Aliyu (Kano State): Chairman, National Educational Research and Development Council (NERDC)
Hon. Yahuza Ado Inuwa (Kano State): Chairman, Standard Organisation of Nigeria (SON); Sanusi Musa, SAN (Kano State): Chairman, Institute of Peace and Conflict Resolution (IPCR); Prof. Al-Mustapha Alhaji Aliyu (Sokoto State): Director-General, Directorate of Technical Cooperation in Africa (DTCA); Sanusi Garba Rikiji (Zamfara State): Director-General, Nigerian Office for Trade Negotiations (NOTN); Mrs Tomi Somefun (Oyo State): Managing Director, National Hydro-Electric Power Areas Development Commission (HYPPADEC); Dr Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria (Kaduna State): Executive Director, Nigerian Integrated Water Resources Management Commission (NIWRMC)”, kamar yadda NewsPoint Nigeria ta ruwaito.

Kazalika, ya bayyana cewa naɗin muƙamin zai fara aiki ne a nan take.

By Babaji