
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana yadda wasu ƴan gaban goshi suka riƙa yin kutsen takardu kai-tsaye duk da tsarin bi ta ofishinsa da doka ta wajabta.
Farfesa Gambari, wanda ya yi aiki a muƙamin daga shekarar 2020 zuwa 2023, ya bayan haka ne a yayin hira da gidan telebijin na Channels, ranar Juma’a.
Ya ce, masu yin hakan a lokacin suna amfani da damar ganawa da shugaban ƙasar ne kai-tsaye, lamarin da acewarsa ya sa suka riƙa miƙa masa takardun.
An naɗa farfesan, wanda tsohon masanin harkar difulomasiyya kuma tshohon wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya ne bayan rasuwar marigayi Abba Kyari, wanda shi ne tsohon riƙe da muƙamin har zuwa watan Afrilun 2020.
A lokacin ne Buhari ya shelanta cewa baki ɗaya harkokin sadarwa ciki har da takardu daga ministoci da ma mataimakin shugaban ƙasa, wajiban ne su biyo ta ofishin Shugaban ma’aikata, yana mai yaba wa Yemi Osibanjo, wanda a cewarsa, ta hannunsa ya ke aiko da takarda.
Ya ƙara da cewa, wasu da dama daga cikin ministoci su kan bi umarnin shugaban ƙasar, saidai wasu kan ta bayan fage.
