Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci Kotun Kolin Nijeriya da ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shigar, na ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Lauyoyin Tinubu ƙarƙashin jagorancin Wole Olanipekun (SAN) ne suka bayyana hakan, wanda a martanin da Atiku ya ɗaukaka, ya buƙaci Kotun Kolin ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da ya shigar na cin zarafi.
A cikin ƙarar da Atiku ya shigar, ya buƙaci Kotun Kolin ta soke hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke kan rashin gaskiya, inda a ƙarshen ta ce ya kasa tabbatar da zarge-zargen aikata ba daidai ba, da kuma rashin bin dokokin zaɓe da ƙa’idojin zaɓe.
Har ila yau, Atiku ya gabatar da wasu sabbin shaidun da ke nuna cewa Tinubu ya buga akardar shaidar kammala karatun digiri na ‘bogi’ daga Jami’ar Jihar Chicago don tabbatar da cewa bai cancanci tsayawa takara ba a ƙarƙashin sashe na 137 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
