Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) Limited, inda ya maye gurbin Mele Kyari. Haka zalika, ya sauke shugaban kwamitin NNPCL, Cif Pius Akinyelure, tare da maye gurbinsa da Ahmadu Musa Kida.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, an bayyana cewa an sauke duka mambobin kwamitin da aka naɗa tare da Akinyelure da Kyari tun a watan Nuwamba na 2023. Sabon kwamitin na da mambobi 11, ciki har da Adedapo Segun a matsayin babban jami’in kuɗi, da wasu wakilai daga shiyyoyin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya ce wannan sauyi yana da matukar muhimmanci wajen bunƙasa ayyukan NNPC, jawo hankalin masu zuba jari, da haɓaka masana’antar iskar gas da tace mai a Najeriya. Gwamnatin sa na da burin ƙara yawan jarin da ake samu daga harkar mai zuwa dala biliyan 30 nan da 2027, da kuma dala biliyan 60 nan da 2030.
Sabon Shugaban NNPC, Injiniya Bashir Ojulari, ƙwararre ne a fannin man fetur, kuma ya rike muƙamai daban-daban a kamfanonin Elf, Shell, da Renaissance Africa Energy. Shugaba Tinubu ya gode wa tsofaffin shugabannin NNPC bisa ƙoƙarin su, musamman a fannin gyaran matatun mai na Port Harcourt da Warri, tare da yi musu fatan alheri a rayuwa.
