Galadiman Kano, Abbas Muhammadu Sanusi ya rasu yana da shekaru 92

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

An sanar da rasuwar Alhaji Abbas Muhammadu Sanusi, Galadiman Kano kuma ɗaya daga cikin masu zaɓen sarki a masarautar Kano. Wani ɗan uwa daga cikin iyalansa ya tabbatar wa da Manhaja cewa marigayin ya rasu ne a daren Talata a gidansa dake unguwar Sagagi, bayan fama da jinya mai tsawo. Sanusi, wanda ya rasu yana da shekaru 92, ya bar mata uku, ‘ya’ya da jikoki da dama.

An haifi Sanusi a ƙaramar hukumar Bichi a shekarar 1933, kuma yana daga cikin mutanen da suka nemi sarautar Kano bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero. Ya kasance cikin majalisar masarautar tun daga shekarun 1950, inda ya riƙe sarautar Wamban Kano kafin a naɗa shi Galadiman Kano a watan Oktoba na shekarar 2014. Sarautar Galadima dai tana da dogon tarihi a masarautar Kano tun zamanin Haɓe kafin jihadin Fulani a 1804, inda ita ce babbar sarauta kafin a ƙirƙiro sarautar Waziri a shekarar 1890.

A halin yanzu, sarautar Galadiman Kano ita ce ta biyu mafi girma a masarautar bayan ta Waziri. Ana sa ran za a sanar da shirye-shiryen jana’izar marigayin nan gaba kaɗan

By ukarofi