“Ilimi abin nema ne tun daga zanin goyo har zuwa kabari”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Makwanni biyu da suka gabata mun kawo muku sharhin littafin ɓarayin Zamani, wanda marubuci Ɗanladi Zakariyya Haruna ya wallafa. A wannan makon za mu kawo muku hirar da marubucin ya yi da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu, game da dalilan da suka sa ya rubuta littafin ‘ɓarayin Zamani’, da kuma nasarorin da ya samu a harkar rubutun adabi. A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Za ka gabatar mana da kanka.
ɗanladi: Assalamu alaikum. Sunana na yanka Zakariyya amma galibi ana kirana Ɗanladi saboda kasancewar an haife ni ranar Lahadi kuma ka san ɗabi’ar Hausawa na sakaya sunan da aka raɗa na wani babba a dangi. To, ni sunan Kakana ne na wajen Uwa. Akwai wasu ƙananan laƙabobin da Baffanni da Kawunnaina ke yi mini, amma dai ɗanladi ɗin ya fi shahara.
Dangane da ayyukana kuwa, ina da ƙwarewa ne a ɓangaren lissafi da binciken hadahadar kuɗaɗe da musanya, wato ni ƙwararren Chartered Accountant ne, kuma mamba a ƙungiyar ƙwararrun Akantoci ta Nijeriya, wato Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN). Haka kuma, ni marubuci ne. Don rubutu ya zame mini wani ɓangare na ayyukana na yau da kullum. Kana iya ce mini Akawu ko Odita ko Marubuci duka ɗaya ne.
Ko za ka gaya mana tarihin rayuwarka?
An haife ni a unguwar Gyaɗi-Gyaɗi cikin birnin Kano, a watan Yuli na 1981, amma na tashi a unguwar Hausawa. Na yi karatu daga sakandare har zuwa matakin digiri na biyu, watau (MBA) a fannin Gudanarwa daga Buɗaɗɗiyar Jami’a ta Nijeriya (National Open Uniɓersity). Haka kuma ina da diploma guda biyu ta fannin nazarin kasuwanci da ilimin sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa. Sai babbar diploma (HND) a ɓangaren nazarin harshen Hausa, da kuma digiri a ɓangaren aikin Akawu. Na soma yin wani digiri a ɓangaren nazarin tsarin banki da tattalin arzikin Musulunci, amma ban kammala ba na jingine shi. Kila nan gaba zan waiwaya na ɗora daga inda na tsaya.
Ina yin rubuce-rubuce cikin Hausa da Inglishi, ina kuma fassara, da kuma ƙirƙirar gajerun labarai, gami da nazarin al’adun Hausawa. Na yi rubuce-rubuce da dama a fannoni daban-daban tare da fassara daga Ingilishi zuwa Hausa. Na rubuta littatafai da dama da kuma ‘yan gajerun labarai.
Wacce gwagwarmaya ka fuskanta lokacin tasowarka game da sha’anin neman ilimi da cigaban rayuwa?
Kamar yadda na bayyana maka a baya, kusan kullum a karatu da neman ilimi nake, tun daga tasowata zuwa yau ɗin nan. Shi ilimi abin nema ne tun daga zanin goyo har zuwa kabari. Wannan ne ya sa nake ta ƙoƙarin neman ilimi a fannoni da dama, musamman inda na fi buɗe ido watau lissafin kuɗi, rubuce-rubuce, da nazarin na’ura mai ƙwaƙwalwa. Baya ga karatu a makaranta, ina yin karatu a duniyar yanar gizo watau internet. Bari na ba ka misali, a lokacin kulle na Kwarona, na yi karatu a intanet wanda ake kira ‘self deɓelopment’ inda na samu shaida a fannoni goma 16 a ɓangarori daban – daban na nazarin kwamfuta da sauransu.
Me ya ja hankalinka a harkar karatu da rubuce-rubuce?
Na samu sha’awar shiga harkar rubuce-rubuce ne daga sauraron labarai daga labarun baka da labaran rediyo irin su Shafa Labari Shuni da Jakar Magori da Kunnenka Nawa? da sauransu. Daga nan sai kuma na soma karance-karancen labarai da jaridu da muƙalu. Daga karance-karancen ne na samu sha’awar rubuta nawa labaran. An ce da jarrabawa jirgin sama ya tashi. Don haka da gwadawa da dagiya gami da nazari dai na samu nake rubutu har yau har magajin gobe.
Za ka iya tuna rubutunka na farko, kuma a kan mene ne?
Rubutuna daga gajerun labarai ya soma. Na kan yi rubutu na karanta kuma na adana shi. Zai yi wuya na iya tuna labari na farko da na rubuta. Amma cikakken littafi na farko da na soma rubutawa shi ne littafin ‘Saura ƙiris’, wanda ke bayani akan wani saurayi da ya ke tamɓelen son wata budurwa da ya san ta fi ƙarfinsa nesa ba kusa ba. Ita kuma ganin girma da martabar zaman tare ya sa ta ƙyale shi har ya zamana saura ƙiris burinsa ya cika a nan ne ya gane ashe ma shifcin gizo ne yake ɗibar sa.
Kawo yanzu ka rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayen su da bitar wasu daga ciki.
Na rubuta littattafai da dama, an wallafa wasu, waɗansu kuma suna nan jibge ba a wallafa su ba. Amma da yardar Allah zan sake waiwayar su na fitar da su ga jama’a. Waɗanda zan iya tunawa a halin yanzu su ne, ‘Saura ƙiris’, ‘Maganin ƙarya’, ‘Ciki da Gaskiya’, ‘Garin Banza’, ‘Lokaci Ya yi’ (Wasan Kwaikwayo), ‘Tekun Labarai’ (Kundin Gajerun Labarai) mai Juzu’i-Juzu’i. Sai kuma Kowanne Gauta, ‘ɓarayin Zamani’, ‘Hanyar Makka’, ‘Duniya Zaman Marina’ (Kundin Gajerun Labarai), da kuma ‘Zuciyar Marubuci’, sai ‘Cikin Duhu’.
Haka kuma an yi haɗaka da ni a rubutun wasu littattafan, fitacce daga cikinsu shi ne, ‘Labarun Dare Dubu Da ɗaya’, wanda muka rubuta tare da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Bukar Mada. A ciki an wallafa guda ɗaya saura mujalladai tara da ke jiran a wallafa su.
Ina da gajerun labarai da dama da nake tunanin haɗe su zuwa littafi. Bari na yi waiwaye ga wasu daga littatafan da na rubuta.
Maganin ƙarya: Labari ne akan rikicin soyayya da zaman doya da manja, da kuma illar zargi da sauransu. A cikin labarin akwai wani saurayi Kamal da ya taka sawun ɓarawo yayin da ya ziyarci gidan surukinsa da ba ya son sa. Zuwan ya zama daidai lokacin da wasu ‘yan ina da kisa suka shiga gidan domin aiwatar da wata manufarsu ga maigidan. Da yake ƙaddara ta riga fata sai ga shi ta ƙare ga wanda bai ji ba bai gani ba. Sai dai a ƙarshe da suka hallara waje guda gaskiya ta bayyana.
Shi kuma, ‘Ciki da Gaskiya’, labari ne akan binciken mai laifi da tabbatar da gaskiya ga wanda ya cancanta. An birkita tunani kan hanyoyin binciken ƙwaƙwaf da irin yadda masu bincike ke ƙoƙari ko akasin haka wajen gudanar da aikinsu. Littafin ya ba da haske game da yadda ake gudanar da bincike, rikicin siyasa, da kuma yadda aka himmatu wajen ɓoye gaskiya. Haka nan, ya nuna ƙarfin ƙuduri da jajircewar jami’an tsaro wajen gano gaskiya duk da cewa suna fuskantar matsaloli masu yawa.
Akwai kuma littafin, ‘Lokaci Ya Yi’, wanda shi kuma wasan kwaikwayo ne da ya shafi al’amuran siyasa, da zamantakewa, da kuma jajircewa. Labarin ya mayar da hankali ne kan Dakta Umar Malami, wani babban likita mai himma wajen yaƙi da rashin adalci da son kawar da cututtukan da suke damun al’umma. Dakta Umar ya gano cewa ruwan sha da ƙasar marmara sun ƙunshi sinadarai masu cutarwa, kuma ya yi ƙoƙari ya wayar da kan jama’a game da haɗarin da ke tattare da shi. Sai dai ƙoƙarinsa ya tafi a banza saboda shakulatin ɓangaro da shugaban ƙaramar hukumar ya yi akan lamarin. Har sai da mai aukuwa ta auku sannan jama’a suka farga cewa lokaci ya yi da gaskiya za ta murƙushe ƙarya.
‘ɓarayin Zamani’ kuwa littafi ne na Hausa wanda ya bincika tasirin fasahar zamani a al’umma, musamman ga matasa. Ya nuna amfaninta da kuma ƙalubalenta, yana ƙarfafa tasirin ilimi da nutsuwa wajen amfani da fasahar zamani. Littafin yana koyar da yadda ake amfani da fasaha ta hanyar da ta dace duk da cewa an yi shi ne ta sigar labari amma dai kam ya zama wani jigo ga sha’anin fasahar intanet yadda mai karatu zai fahimci wasu abubuwa cikin sauƙi da yadda za a kare kai daga miyagu masu sata a intranet, wato hackers.
Waɗanne nasarori ko matsaloli ka fuskanta a harkar rubutu?
Rubutu kam ya yi mini rana ba kaɗan ba. Ta dalilinsa na san jama’a sosai kuma jama’a sun sanni. Na gamu da mutanen kirki masu son taimako da ƙarfafawa matasa. Sun ba ni shawarwari masu kyau da suke tasiri gare ni a duk inda na shiga. Haka kuma na samu damar haɗuwa da sauran marubuta da masu sha’awar adabi, wanda ya ƙara ƙarfafa ni da kuma ba ni damar koyo daga ƙwarewar su.
Har ila yau ga ɗimbin kyaututtuka da fatan alheri daga masoya da magoya baya. Har ila yau na samu nasarori a gasar rubutu da dama watau kamar gasar Duniyar Marubuta (2013), Makarantar Malam Bambadiya (2014), Gasar Tsangayar Gusau ta Gusau Institute (2018), Pleasant Library (2019), Architecth Dangiwa (2021) da kuma Gasar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano (2024). Baya ga ƙananan gasanni da sauran ababe masu ɗimbin yawa.
ƙalubale kuwa, baya ga matsalolin gama gari da ɗaukacin marubutan Hausa ke fuskanta, wato kamar rashin isassun kuɗin wallafa, da yawaitar satar fasaha da kuma raguwar son karatun littatafai da yanzu duka an koma tsarin dijital. Ni kuma ina fuskantar ƙarancin lokaci, kamar yadda a yanzu ba na samun lokacin da zan yi rubutu kamar yadda nake yi a baya. A baya, duk da ƙarancin bincike, na kan iya rubuta littafi guda a ‘yan kwanaki ƙalilan. Yanzu kuwa ga wadatar hanyoyin gudanar da bincike, amma lokaci ya hana ni yin kataɓus. Shi rubutu yana buƙatar lokaci mai yawa da kuma jajircewa, idan ka rasa lokacin zaunawa ka yi tunani mai kyau kuma ka rubuta, sai ka zama tamkar ragon da aka yi wa dabaibayi.
Me ya ƙarfafa maka gwiwa wajen rubuta littafin ‘ɓarayin Zamani’?
Na yi tunanin rubuta ‘ɓarayin Zamani’ ne domin faɗakarwa cikin nishaɗi ga al’ummar Hausawa, musamman yadda za su kiyaye kansu daga afkawa sharrin masu aiki da na’urori domin aiwatar da satar dukiya ko wani keɓantaccen sirri. Kamar yadda amfani da intanet ya yawaita, haka ma damfara ta intanet ta zama ruwan dare. Wasu na amfani da wannan fasaha ta zamani domin ci da gumin waɗansu. Na yi nuni da cewa, a da, ɓarayi suna amfani da makamai da ƙarfi wajen aikata laifinsu, amma a wannan zamani, suna amfani da wayo, fasaha, da ilimi wajen aikata satar tasu musamman a yanar gizo.
Don haka wajibi ne kowa ya naƙalci yadda zai kare kansa daidai gwargwado. Na tabbata duk wanda ya karanta wannan littafi da idon basira zai samu wani abu da zai amfana da shi game da tsare sirrinsa a duniyar gizo. Duk da cewa kullum ana fito da sabbin dabarun sata a intanet, wannan littafi na iya kasancewa hanjin giwa mai dauke diyan amfani da yawa.
Wanne tasiri littafin ‘ɓarayin Zamani’ ya yi ga masu karatu lokacin da ya fita?
Lokacin da na rubuta littafin, sai na ga tamkar ya zame mini alaƙaƙai, ƙashin bakin tukunya. Saboda sarƙaƙiyar da ke ciki da kuma wasu irin kalmomi da ba a saba da su ba. Kuma kasancewarsa kusan littafin Hausa na farko da ya yi tsokaci akan jigon matsalolin intanet watau Cyber Security, sai na kasa samun wuraren da zan ƙara samun haske sosai akan yadda masu karatu ke iya fahimtar saƙon. Da taimakon wasu malamaina da abokan aiki na iya samun fassara ma’anar wasu kalmomin, kuma na samu na daidaita labarin yadda zai yi armashi da daɗin karantawa.
Yayin da littafin ya fito sakamakon gasar Cibiyar Gusau Insitute, sai mutane suke ta rububin karantawa, kuma suke nuna jin daɗinsu da yadda aka yi nuni cikin nishaɗi. Duk wanda ya karanta sai ya ƙaru da wani muhimmin saƙo da zai iya kare kansa daga miyagun da ke sata a kafafen sada zumunta na zamani. Haƙiƙa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, kuma haƙa ya cimma ruwa dangane da manufar rubuta littafin.
Shin an taɓa damfararka ko cutar da kai ta hanyar fasahar zamani, da ya ja hankalinka wajen rubuta littafin ɓarayin Zamani?
Za mu dakata anan, inda za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar Allah. Marubucin zai soma da ba mu amsar wannan tambayar kafin mu je zuwa ga wasu.
