Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gudanar da taron gangamin bikin Sallah tare da magoya bayanta a Ihima, Kogi ta tsakiya, duk da umarnin gwamnatin jihar na hana irin wadannan gangamin. Tun da safiyar Talata, magoya bayanta daga ƙananan hukumomi biyar na yankin sun taru domin tarbar sanatar da ke wakiltarsu a majalisar tarayya ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Waƙar gargajiya da nishadi sun kasance a wurin yayin da ake jiran isowarta, inda daga bisani ta iso cikin wani farin jirgi mai saukar ungulu, lamarin da ya haddasa murna da jin daɗi daga magoya bayanta.
Sanata Natasha ta bayyana cewa bata karya doka ba, domin ba taron siyasa suke ba, illa dai dawowarta gida domin bikin Sallah tare da al’ummarta. Ta ce: “Mun ji jiya ana cewa an haramta taruka da gangami, kuma an ce za a rufe hanyoyi domin hana shiga jihar. Amma wannan ba lokacin siyasa bane, kuma ba yaƙin neman zaɓe muke ba. Ina nan ne kawai domin yin Sallah tare da mutanena.”
A ranar da ta isa, gwamnatin Kogi ta bayyana cewa an hana taruka saboda dalilan tsaro, tare da sanya dokar hana fita a yankin Okehi. Haka zalika, ‘yan sanda sun buƙaci sanatar da ta soke taron. Duk da haka, ta ce babu wanda zai hana ta dawowa gida. Kafin taron, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, da laifin duk wani abin da ka iya faruwa na rashin tsaro. Wannan ya biyo bayan dakatarwar da aka yi mata a majalisar dattawa da kuma ƙoƙarin tsige ta daga kujerarta.
